Daga Rabiu Ali Indabawa
Wasu da ake zargin masu satar mutane ne da suka addabi yankin Yolde Pate da ke Karamar Hukumar Yola ta Kudu a Jihar Adamawa a jiya, sun sace matar da dan wani jami’in tsaro na tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.
An yi zargin cewa masu garkuwa da mutane wadanda suka addabi yankin, sun gudanar da aikinsu na kusan minti 30. Shaidun gani da ido sun yi zaton cewa sun zo ne don kare lafiyar Atiku, amma sai suka tafi da matarsa da dansa a lokacin da ba su ganshi ba. Wani ganau ya shaidawa jaridar The Nation cewa;
“Masu garkuwar sun yi amannar cewa jami’an ‘yan sanda, kasancewar suna da kusanci da Atiku, za su samu kudi, don haka suka neme shi amma suka tafi da matarsa da dansa lokacin da ba su same shi ba.”
“Mu na son mazauna yankin su taimaka wajen ba da bayanai kan lokaci kuma masu amfani da za su iya taimakawa wajen bin diddigin wadanda suka aikata laifin.”