Gungun ‘yan bindiga sanye da kayan jami’an tsaro sun yi wa motar fasinja kirar bas kwanton bauna a a kan hanyar Gurbin Baure da ke karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da matafiya masu yawa, lamarin ya faru ne da yammacin jiya Talata; majiyoyi sun ce ‘yan bindigar na sanye ne da kayan sojin da na ‘yan sanda, inda suka kafa shinge mai kama da shingen bincike na jami’an tsaro.
Wani matafiya dan garin Jibiya ya shaida cewa; ‘Gungun ‘yan bindigar sun sanya shingen bincike ne a kan hanyar inda suka yi awon gaba zuwa cikin daji da dukkan matafiyan da suke cikin bas din.’
Jami’an ‘yan sanda jihar Katsina basu kai ga tabbatar da faruwar lamarin ba, sannan zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance adadin matafiyan da aka yi awon gaba da su ba, garin Jibiya ya na kan iyaka ne da Jamhuriyyar Nijar.