Dakta Azubuike Joel Iheanacho, babban daraktan asibitin Peace dake Anyigba,wanda wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranan asabar data gabata ya samu kubuta kuma tuni ya hadu da iyalansa.
Kakakin rundunar yan sandar jihar Kogi, DSP Williams Ayah ne ya tabbatar da hakan a yayin da ya ke zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP Ayau ta wayar salula a jiya Talata a garin Lokoja.
Ya ce, ’yan bindigar sun sako likitan ne a ranan litinin da misalin karfe 9 da 40 na dare,
DSP Ayah yace kokarin yan sanda tare da hadin gwiwar yan banga dake garin Anyigba ne ya kai ga kubutar da shi.
Kakakin rundunar yan sandan har ila yau ya shaida wa wakilimmu cewa rundunar na samun labarin sace Dakta Iheanacho, nan da nan kwamishinan yan sandan jihar Kogi, CP Edeh Ayuba ya baiwa babban jami’in yan sanda mai kula da yankin( DPO)umurni daya gabatar da faraurar masu garkuwa da jama’ar don ganin sun sako likitan.
A kan nema DSP Williams Ayah ya baiwa jama’a tabbacin cewa rundunar yan sandan zata ci gaba da farautar yan bindigar wadanda suka ranta na kare, har sai ta kai ga damke su don su fuskanci shari’a.
A ranar asabar data gabata da misalin karfe 9 da 30 na dare ne, masu garkuwa da jama’ar suka afka gidan Dakta Azubuike Joel Iheanacho a garin Anyigba dake karamar hukumar Dekina, inda suka yi awon gaba da shi a yayin da yake tare da uwargidansa da kuma wani dan uwansa cikin motarsa a kofar gidansa.