Wani babban Limami a kauyen Kwawaran Rafi da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Malam Danleeman Isah ya gamu da fushin ‘yan bindiga dadi inda suka hallakashi biyo bayan jawabansa da yake yawan yi na suka a kan ‘yan fashi da makami.
A wata sanarwar da kwashinan kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar a karshen mako, ya nuna cewa makasan sun aikata danyen aikin nasu ne a lokacin da suka farmaki kauyen.
Ya shaida cewa, kashe Malamin bai rasa nasaba da yadda malamin ke suka da tur da ayyukan ‘yan fashi da masu garkuwa mutane da satar shanu.
Sanarwar ta ce; “Yan fashin sun wuce kai-tsaye zuwa gidan Malam Danleeman Isah, kuma kamar da ma abin da ya kai su kenan, suka harbe shi tare da barin wurin ba tare da sun dauki komai ba ko kuma garkuwa da wani.”
Sannan, Aruwan ya tabbatar da mutuwar Sarkin Yakin Godogodo mai suna Yohanna Abu, bayan wasu miyagu sun kai wa garin Nisama hari da ke karamar Hukumar Jema’a a daren ranar Juma’a.
Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Charles Audu ya rasa ransa a harin sannan suka yi garkuwa da wani mai suna Mr Abu.