Muhammad Awwal Umar" />

’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Fasinjoji A Neja

Fasinjoji

Kimanin mata fasinjoji talatin da biyu ne ‘yan bindiga su ka yi awon gaba da su tsakanin Kundu da Zungeru a yammacin lahadin nan da ya gabata.

Lamarin da ya faru da motar sufuri mallakin gwamnatin jiha ( NSTA) mai lamba takwas, a lokacin da ya dauko fasinja daga garin Rijau da Kontagora zuwa Minna.

Wani mazaunin kauyen Garin-Gabas da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana ma wakilin mu a lokacin da suke gudun tseren kaucewa fada wa hannun maharan, yace maharan sun shigo yankin Yakila kimanin kwana uku ke nan suna karakaina a yankin kuma an sanar da gwamnati da jami’an tsaro amma ba wani matakin da aka dauka akai.

“Da ma idan suna son gudanar da harkokin su, haka suke shigowa da yawa har yankunan mu suna hidimar su kwatsam sai ka ji sun yi aika-aikar su, kuma sau tari mu kan sanar da shugabannin mu dan su sanar da gwamnati.”

Wasu fasinjojin da sauran matafiya sun nuna takaicin su kan yadda jihar Neja ke kokarin komawa sansanin ‘yan bindiga dadin da ke aiwatar da ayyukan su akan hanyoyin da wani lokaci kan shafi mutanen karkara da ke zaune shakara da shekaru a wadannan wuraren.

Zuwa hada labarin dai ba wani tattaunawa tsakanin maharan da iyalan wadanda ake garkuwa da su da wannan harin ya rutsa da su din.

Gwamnatin jiha dai ta sha bayyana cewar bakin kokarinta na kawo karshen ayyukan maharan a fadin jihar, wanda jama’a sun kasa tabbatar da gaskiyar gwamnatin akan wannan ikirarin da ta ke yi ganin yadda a kullun sai an samu labarin kai hare-hare a wasu yankunan jihar.

Hanyoyin da abin ya shafa sun hada da Birnin-gwari ta jihar Kaduna zuwa Pandigari zuwa Kagara a cikin karanar hukumar Rafi, sai Kwakuti zuwa Paiko a karamar hukumar Paikoro, da hanyar Tegina zuwa Zungeru da ke iyaka da karamar hukumar Rafi zuwa Wushishi, da kananan hukumomin Munya da Shiroro wadanda ke iyaka da jihar Kaduna.

Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jiha, Malam Ibrahim Balarabe a wani taron sabunta rajistan jam’iyyar APC da ya gudana a Kagara ta karamar hukumar Rafi, yace mai girma gwamna a tsaye yake wajen hada kai da jami’an tsaro wajen ganin an kawo karshen wannan lamarin, inda yace a kowani lokaci kofar gwamnatin jiha a bude ta ke wajen bada shawarwarin hanyar da za a kawo karshen yin garkuwa da kai hare-haren maharan a jihar baki daya.

Matakan da gwamnati ke dauka yanzu ba sai ta fito ta bayyana su ba saboda abu ne na sirri, amma tabbas gwamnati na bakin kokarinta akai.

Exit mobile version