Daga Rabiu Ali Indabawa,
Wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da Alhaji Ibrahim Ahmed mai shekaru 91.
Tsohon shine Dagacin Kauyen Kunduru da ke Yankin Karamar Hukumar Kankia ta Jihar Katsina.
Sun sace mahaifin babban sakataren gwamnatin jihar Katsina, Kashimu Ibrahim ranar Juma’a. Wani mazaunin yankin ya ce an sace dagacin ne a daren Juma’a yayin da ‘yan bindiga suka tsinkayi gidan basaraken da ke Kunduru kuma suka yi awon gaba da shi. Kamar yadda majiyar ta ce, wanda aka sace din shi ne mahaifin Kashimu Ibrahim, daya daga cikin manyan sakatarorin gwamnatin Jihar Katsina. Amma kuma, daya daga cikin ‘ya’yan basaraken ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a garin Katsina, LEADERSHIP ta tabbatar. Dan Basaraken wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindiga sun shiga kauyensu a kan babura inda suka kai musu hari har suka yi nasarar sace mahaifin nasu.