Hukumar ‘yan sandan jihar Nasarawa sun tabbatar da an yi garkuwa da tsohon ministan kwadago, Mista Hussaini Akwanga.
Tsohon ministan ya yi aiki ne a zamanin mulkin Obasanjo, sai dai an cire shi saboda zargin badakalar makudan kudade.
Mai Magana da yawon rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa DSP kennedy Idrisu, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a yau Laraba, shi dai tsohon ministan an sace shi ne a gidan gonar sa da ke hanyar Wamba a garin Akwanga.
Bayan samun rahoton sace tsohon Ministan, Idrisu yace kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya tura jami’an tsaro yankin domin kubutar da Hussaini Akwanga.