‘Yan Bindiga Sun Zama Kwastominmu Na Kut, Inji Mai Saida Buredi Da Ke Musu Safaran Buredi

’Yan Bindiga

Daga Khalid Idris Doya

Daya daga cikin masu sana’ar saida Buredi da aka cafke suna safaran buredi wa ‘yan bindiga, ya shelanta cewa ‘yan bindigan da suke cin karensu babu-babbaka a Kaduna sun kasance kwastominsu na kwarai kuma na kut da suke samun riga sosai a wajensu.

Masu sana’ar Buredi su uku da ‘yan sanda suka cafke sun bayyana da bakinsu cewa suna safaran buredin ga ‘yan bindiga.

‘Yan bindigan da suke garkuwa da mutane a Damari, Kidandan da Awala da suke Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Wadanda ake zargin sun kuma kai ‘yan sanda zuwa gidan buredin da suke yin sana’ar tasu.

Daya daga cikinsu na cewa, “Ni mazaunin kauyen Galadimawa ne, ina da aure matana biyu ina da ‘ya’ya uku. Na fara sana’ar yin Buredi a 2018.”

“Ni da mai kabu-kabu ne don ina sana’ar Achaba ne, na rasa Mashin din da nake sana’a ne a wani lokacin da ‘yan bindiga suka kawo mana hari a wani lokacin baya can. Wani lokaci bayan da na zauna bana komai, daya daga cikin ‘yan uwana Mustafa Magaji ya sameni ya ce na zo muke zuwa wajen buredi domin nake samun ‘yancin da zan rayuwa, nan take na fara sana’ar Buredi.

“Lokacin da na fara ana biyana naira N21,000 zuwa yanzu na samu likafa ta cilla ina samun N400,000 duk wata. Sana’ata ta ingantu ta bunkasa ne a lokacin da na fara safaran Buredi ina kai wa ‘yan bindiga. An haifeni a Galadimawa kuma a nan na tashi na san matasanmu da daman gaske da suka yanke shawarar zama ‘yan bindiga.

“Yankinmu na da kyakkyawar alaka da su saboda sun daina kai mana hari. Da farko sun fara kawo mana hare-hare amma daga baya shugabannin yankinmu suna fahimtar da su cewa mu ba matsala bane a garesu, domin mu talakawa ne wadanda muke buga-bugar yadda za mu rayu.

“Wannan ne ya sanya suka rage kai hari wa yankinmu kuma suka samu damar kwasan wasu. Na kasance mai zirga-zirga zuwa sayar da buredi har ckin dazuka”

Da yake bayanin yadda suka fara haduwa da ‘yan bindiga, ya bayyana cewar, “A irin tafiye-tafiyen da na ke yi a wani lokaci a 2019 na hadu da wani mai suna Mohammed ya sayi guda goma sannan ya amshi lambar wayata. Na saida masa kan kudi naira dari biyu ga kowanne a maimakon naira 170 da ake saidawa a kasuwa.

“Tun daga wannan ranar ya kirani ya ce lallai buredin ya masa dadi sosai yana son na kawo mana guda 20.

“Da na kai masa guda 20 din, sai na gamu da wasu uku sai suka bukaci nake kawo musu Buredi da yawa za su ke saya. Nan dai na musu korafin cewa ba mu da kudi da yawa a hannunmu da zan ke kawo musu da yawa, sai suka ce za su ke biyana ma tun kafin na dauko Buredin.

“Sun fara da bani dubu ashirin sannu a hankali suka koma zuwa naira dubu hamsin duk rana guda. Bayan na fara lissafi idan na cire kudaden kayan a mako guda na kan samu kamar N150,000.

“Muna da wani wajen da muke haduwa da su a boye domin na ki amincewa na shiga cikin daji inda suke. Wurin ma ba mu iya shiga da mota. Kwata-kwara basu min barana muna kasuwancinmu ne kawai da su.

“Sun san jama’a suna gudun su, amma ni da suka fara da ni sai suka rike ni hannu biyu-biyu suna karfafan na ke cigaba da kawo musu Buredin. Ban san sana’arsu garkuwa da mutane bane, illa dai kawai muna kasuwanci a tsakani kuma muna samun riba mai tsoka.

“Ma’aikata na ne ‘yan sanda suka kama a hanyar da suke dawowa bayan da suka kai wa ‘yan bindigan Buredi, sannan sun kawo ‘yan sanda zuwa gidan Buredin nawa.”

Exit mobile version