Daga Abubakar Abdullahi, Lafia
Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da suka zo sata a gidan burodin Romantic da ke Lafia, sun harbe daya daga cikin jami’an ‘yan sanda masu gadi a gidan burodin mai suna Enojo Paul har lahira.
Wasu shaidu da lamarin ya auku a kan idonsu, sun shaida wa LEADERSHIP A YAU cewa, ‘yan fashin su hudu ne suka zo gidan a cikin wata mota karama kirar Camry mara lamba, inda biyu daga cikinsu suka shiga cikin gidan burodin sannan guda ya koma bakin hanya ya ci gaba da harbi a iska don razanar da jama’a, sai direbansu da ya kasance zaune cikin mota rike da sitiyari.
Shaidun kara da cewa, ‘yan fashi biyu da suka shiga gidan burodin ne su kwashe makuddan kudi a gidan yayin da dansandan da ya yi yunkurin dakile ‘yan fashin, wato Enojo Paul suka harbe shi har lahira.
Wata ma’aikaciyar gidan burodin wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa, suna cikin hada-hadar kasuwanci ne kwatsam sai suka ji harbin bindiga da shigowar ‘yan fashin cikin gidan burodin. Ta bakinta, “Muna ciki sai muka ji kara mai karfi, ni na dauka fashewar tayar mota ce, ba a jima ba na sake jin harbi na biyu sai na ce kai wannan lamari ya fi karfin fashewar tayar mota”.
Ta ci gaba da cewa, “Ganin haka sai muka ruga can ciki, shigowar ‘yan fashin ke da wuya sai suka umurci wadanda suka zo sayen burodi da su kwanta a kasa, sannan suka wakilta daya daga cikinsu kwatomomin namu ta kwashe kudi daga inda ake ajiya ta zuba musu a leda ta mika musu”.
Kazalika ta ce, daga bisani ‘yan fashin suka je kofar ofishin manajan gidan burodin suka yi ta dukar kofar a kan ya bude bude musu kofa amma ya ki, ganin haka sai suka fice suka yi tafiyarsu.
A yayin da wakilinmu ya ziyarci gidan burodin, ya gana da manajan gidan wanda dan kasar China ne, sai dai ya ki ya bayyana sunansa yana mai cewa yana cikin dimuwa na abin da ya farun, inda ya ce, “Sata da ‘yan fashin suka yi ba shi ne ya fi damuna ba, abin da ya fi daga mini hankali shi ne rasa rai na jami’in dan sanda da aka yi”.
Ya ce sau biyu kenan ana aikata masa irin wannan. A cewarsa “An yi min irin wannan a Maiduguri, ga shi an sake aikata min a nan, ina mai kira ga gwamnati da ta karfafa tsaro a ko’ina domin hana faruwar irin wannan lamarin”.
Da kammala fashin, ‘yan fashin sun shiga motarsu suka bi ta hanyar Unguwar Jaba suka arce.
Da yake zantawa da LEADERSHIP A YAU mahaifin marigayin wanda shi ma tsohon dan sanda ne, Paul Ikana, ya bayyana kaduwarsa da yadda aka hallaka masa da, tare da bayyana marigayin da nagari mai biyaya ga iyayensa da kuma girmama kowa. A cewar mahaifin, “Da faruwar lamarin an kira ni, sai dai kafin na wurin an rigaya an wuce da shi zuwa asibiti. Na bi su zuwa asibiti na samu yaron nawa da likitoci a kansa yana numfashi sama-sama ba a jima ba ya ce ga garinku nan. A kan idona ya cika”.
Da yake tabbattar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Idrisu Kennedy ya ce, lallai hakan ya faru kuma da faruwar lamarin rundunar ta shiga bincike. “Mun samu labarin ‘yan fashi sun shiga wani gida a bayan Lafia East mun tattara jami’anmu zuwa wurin, muna can ne sai muka sake samun labarin ana fashi a gidan burodin sai dai kafin mu isa sun ranta a na-kare”, in ji Kennedy.
A karshe, Kennedy ya bayyana cewa rundunar tana bincike kuma ba za ta yi kasa gwiwa ba har sai ta kai ga kama wadanda suka aikata aika-aikar a kuma hukunta su.