Connect with us

JAKAR MAGORI

’Yan Fashi Sun Kashe dan Shekara 52 Ta Hanyar Azabtarwa A Legas

Published

on

Wasu da ake zargi ‘yan fashi da makami ne sun afkawa wani mutum mai shekaru 52, Olumuyiwa Akinfenwa, a yankin Egbeda na jihar Legas, sun kashe shi har lahira ta hanyar azabtarwa.

Wakilinmu ya samu labarin cewa an gano Akinfenwa, wanda ke zaune a Peace Estate, Baruwa a yankin Ipaja na jihar, an gano shi yana kwance a jininsa a kan titin Adepeju, Egbeda, bayan harin ‘yan fashin.

A cewar ‘yan sanda, maharan sun kai hari ne a ranar 17 ga Yuni da misalin tsakar dare kuma an gabatarwa da ‘yan sandan yankin Shasha rahoton afkuwara lamarin.

Wani rahoton ‘yan sanda da wakilinmu ya samu, ya ce, “Magana ce ta wanda ake zargin an kashe. daya daga cikin mazauna yankin ya zo ofishinmu kuma ya ba da rahoton cewa wanda aka kashe mai shekaru 52 da haihuwa an yi tadukansa ne da daddare a kan titin Adepeju,inda ake zargin wasu mutane da ba a tantance ba. Amma mun yi imanin maharan ‘yan fashi da makami ne.

“Ya na kwance a kasa, babu mataimaki, a yayin da tawagar jami’amu ta isa wurin da aka aikata laifin, mun dauki hotuna, daga nan aka dauke shi zuwa ga asibiti. Ko da zuwa isa asibiti likita ya tabbatar da ya mutu. A halin yanzu an dauki gawar kuma an ajiye ta a Babban Asibitin Ikeja don gwaji gami da ci gaba da Bincike don kama wadanda ake zargi da aikata laifin. ”daya daga cikin mazauna unguwar mai suna, Akin Semiu, ya shaidawa wakilinmu cewa, an garzaya da mutumin asibitin koyarwa na Ikeja dake Jihar Legas, amma kafin a karasa crai ya yi halinsa.

Ya ce, “Bai zauna a yankinmu ba. Sai dai zai iya kasancewa Semiu yana kan hanyarsa ce ta zuwa gidansa. An yi imanin cewa zai dawo daga ne daga aiki wadannan mutanen dai suna biye da shi ne. An bayar da rahoton sun yi masa fashi daga baya kuma sun azabtar da shi, suka kashe a nan.

“Ya kamata ‘yan sanda su yi bincike mai zurfi a kan wannan lamarin, saboda duk wanda ke bin wannan titin a halin yanzu yana cikin fargaba, kuma yana da fatan ganin an bi diddigin wannan kisan.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da kisan, yana mai cewa an mika batun zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar, Yaba, domin ci gaba da bincike.

Ya ce, “’Yan sanda sun fara bincike don gano musabbabin faruwara lamarin, An gayyaci mutane biyu don yin tambayoyi. Amma har yanzu ba a kama wanda ake zargi ba. Yanzu an canza lamarin zuwa SCID saboda masu binciken za su iya gano yanayin. ”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: