Rabiu Ali Indabawa" />

‘Yan Fashi Sun Mika Makamansu Ga Gwamnatin Nijar

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Wasu ‘yan fashi da makami a Jihar Agadez da ke Jamhuriyar Nijar sun mika wa gwamnati tarin makamai da ke hannun su a karkashin wani shiri na yi musu afuwa.

Bikin mika makaman ya gudana ne a karkashin jagorancin Ministan cikin gida na Jamhuriyar ta Nijar Bazoum Mohammed.

Wannan dai shi ne karo na uku cikin kasa da shekara guda, da ‘yan fashi da makami su ke mika makamai ga hukumomin kasar.

Makaman sun hada da manyan bindigogi masu sarrafa kansu, makaman roka da kuma alburusai masu tarin yawa.

Mutane sama da 30 ne suka mika makaman ga gwamnati, tare da shan alwashin cewa za su bai wa jami’an tsaron kasar gudunmawa wajen tabbatar da doka da oda.

Exit mobile version