Idris Aliyu Daudawa" />

’Yan Fashi Sun Soka Wa ’Yar Kasuwa Wuka A Delta

Wata mata wadda take da matsakaitun shekaru wadda kuma sunanta, Beatrice Omoroghene, a farkon safiyar ranar Lahadi ce, wasu ‘yan fashi da makamai suka kai mata samame, suka kuma kwace dukkan abubuwan da duk ta mallaka, wadanda kuma suyka hada da wayoyinta guda biyu, sai kuma kudade da suka kai Naira N75,000, a wani wuri wanda ake kira Abraka cikin jihar Delta.
Beatrice wadda ta yi magana da manema labari a wurin da take, a farkon safiyar ta Lahadi ta bayyana cewar ” Su ‘yan fashin sun shigo gidan da take zauna ne, da farkon safiyar, ina yin waya ne, sai suka tsaya bakin Kofa, suna kira na, cewar in bude kofa, sai na roki wani makabci na ya taimaka mani, su ‘yan fashi da makami ne, lokacin da suka shigo gida na a unguwar gidaje na Ekrejeta a gundumar Abraka, sai sukan fara harbe – harbe a sama, kafin su kawo wurina su bukaci cewar na basu wayoyi na daga nan na basu, amma sai na lura daya daga cikin ‘yn fashin yana fushi, lokacin da nake rokon su, sai ya matso kusa dani ya yanke ni a baki na, daga na kuma sai jin ya fara zubo mani, amma da yake su hudu ne, ba zan iya fuskantar su ba, daga nan kuma sai suka amshi Naira 75,000 kafin su fita daga cikin gidan, daga nan ne kuma sai ta kai ma ‘yansanda rahoton al’amarin zuwa ofishin ‘yasanda na Abraka.
Amma kuma sai babban jami’i safritanda na ‘yansanda CPS Ahmed Hassan, da kuma jami’in ‘yansanda na ofishin Abraka, ya tabbatar da aukuwar shi al’amarin, ga manema labarai a wurin da abin ya auku, ya kuma bayyana cewar su ‘yan fashi da makamin sun yi ma ita matar sata, na wayoyinta, da kuma kudade Naira N75,000 inda kuma ya ci gaba da bayanin cewar su ” ‘Yansanda suna kan farautar ‘yan fashin, za kuma su tabbatar da an kama su nan bada dadewa ba.
An dai samu bayanan cewar lokacin da matar take rokonsu kada su kwace mata, su abubuwan da take dasu, musamman ma wayoyinta biyu, da kuma kudade Nairaf N75,000, sai daya daga cikin ‘yan fashin ya matsa kusa da ita, ya kuma yanke ta abaki. Kafin su fita daga cikin gida suna harbe- harbe, cikin sauri da yin harbi ta sama..
Da take kara yin jawabi Beatrice ta bayyana cewar daga baya an kai ta wani asibiti na kusa, inda a halin yanzu ake kulawa da ita zuwa yanzu, ta kuma yi kira ga jami’an tsaro da cewr su tabbatar da sun kamo su.
Mazauna garin Abraka a cikin wannan lokaci suna barci ne da ido daya, ganin yadda ake ta yawan kai masu harin fashi da makami a wurin, amma kuma sai shi CSP Hassan, ya basu tabbacin cewar su ‘yansanda sun sha alwashin kare su daga aukuwar ire-iren wadannan hare- haren da kuma dukiyoyin su.

Exit mobile version