Sabo Ahmad" />

‘Yan Fashi Sun Yi Wa Tsohon Hadimin Ambode Fashi A Bainar Jama’a

Wasu ‘yan fashi da makami sun farwa tsohon hadimin gwamnan jihar Legas Ekene Okoro a daren Laraba larabar da ta gabata a cikin motarsa a kan babban titin Oshodi zuwa Apapa. Okoro, wanda ya yi wa tsohon gwamnan Legas Akinwunmi Ambode aiki a matsayin babban Sakataren yada labarai ya fada hannun ‘yan fashi ne kusa da Cele Bus Stop a hanyarsa ta zuwa Ango Palace da misalin karfe 9:35 na dare.

‘Yan fashin sun samu sukunin gudanar da mummunan aikinsu ne sakamakon cinkoson motocci da aka samu a hanyar. ‘Yan fashin sun sace masa agogo da wayar salula da kuma wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba. Okoro ya ce ‘yan fashi da makamin sun far wa sauran motocin da ke kusa da motarsa bayan sun gama yi masa fashin.

“Bayan sun gama da ni, sun ba ni umurnin in wuce gaba. A wannan lokacin na yi tunanin suna son su yi amfani da ni ne domin su yi wa sauran motocin da ke baya na fashi. “Da na lura hankalinsu ya koma kan motoccin da ke baya na, sai na yanke shawarar komawa cikin mota na saboda in tsere amma da na lallaba na shige cikin motar sai na ga ashe sun dauke makulan motar,” inji Okoro. A yayin da ya ke hira da manema labarai bayan ya sabunta layin wayansa.

Okoro ya ce jami’an ofishin MTN sun fada masa shi ne mutum na hudu da ya zo sabunta layin wayarsa a jiya shekaran jiya Alhamis. Ya yi fatan jami’an tsaro za su dauki mataki kan bata-gari da ke yi wa mutane fashi a hanyar.

Exit mobile version