’Yan Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Kakakin Hukumar Shige Da Fice

Neja

Daga Khalid Idris Doya,

An samu rahoton da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kakakin hukumar shige da fice (NIS) reshen shalkwatar hukumar da ke Edo, Misis Bridget Esene a yayin da take hanyarta na dawowa daga coji a ranar Lahadi.

An ce masu garkuwan sun yi awun gaba da ita ne a lokacin da take kan hanyarta na zuwa wajen bauta da sanyin safiyar ranar Lahadi a yankin Ikhueniro da ke daf da titin Agbor a birnin Benin ta jihar, an ce sun yi dirga da ita sosai kafin daga baya suka sha karfinta inda suka turata cikin mota da karfin tsiya tare da guduwa da ita zuwa maboyarsu da ba a sani ba.

Ya zuwa lokacin hada labarin nan ba a samu wani bayanin cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalanta kan kudin fansa ba.

Majiyar daga hukumar Immigration ta tabbatar da faruwar lamarin da cewa, “An yi garkuwa da ita ne a kusa da harabar cocin da ke kan hanyar Agbor jiya da safiya (Ranar Lahadi kenan). Sun tafi da ita zuwa wani wajen da ba a sani ba, kuma har zuwa yanzu masu garkuwan ba su yi magana da iyalanta ba.

“An samo motarta da aka yasar a kan hanyar Agbor, mun fahimci cewa masu garkuwan sun ce da ita ta hanyar Benin Auci ne,” a cewar mai bada bayanin.

Exit mobile version