‘Yan Gudun Hijira 79 Suka Amfana Da Shirin Kamfanin PAN

Daga Abubakar Abba, Kaduna

An yaye ‘yan gudun hijira su 79 karo na farko da kamfanin (PAN) ya horar dasu ƙarƙashin shirin sa na (TSAP) na rage taluci.

A jawanbin sa a wurin yayen, Manajin Daraktan Kamfanin Ibrahim Boyi, “mun sada waɗanda aka yayen ɗin don samar ma su da dama a kamfanin da sauran kamfanunnuka musamman Kamfanin rukunonin wanda ya ɗauki wasu daga cikin waɗanda aka yaye ɗin aiki.

Boyi ya ce, yana da kyau aga ‘yan gudun hijirar mazan su da matan su, suna bada tasu gudunmawar wajen ciyar da tattalin arzikin ƙasar nan gaba da tallafawa iyalan su da kuma al’umominsu.

 

Exit mobile version