’Yan Gudun Hijira 8,000 Sun Koma Gidajen Su A Bama –NEMA

Shugaban shiyyar Arewa maso Gabas na hukumar taimakon gaggawa ta, NEMA, Bashir Garga, ya ce, jimillan ‘yan gudun hijira 8000 ne suka koma gidajen su na gado a garin Bama.

Bashir, ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Maiduguri a karshen makon nan, inda ya ce, kimanin magidanta 1200 ne suka dawo bayan shekaru uku suna zaman gudun hijirar.

Ya ce, tun da farko sama da mutane 36,000, ne suka nu na aniyar su ta komawa gida, amma sai hukumomin na SEMA da NEMA, suka ce sai dai su dawo rukuni-rukuni, domin su sami daman aikin tantance baragurbi a cikin su.

“Ya zuwa yanzun, akalla mutane 8000 ne suka koma gidajen na su, bisa kidayar mutane shida a kowane gida za mu iya cewa, magidanta 1200 kenan. In fayyace maku sosai, baya ga mutanan Bama da suka dawo, muna da wasu ‘yan gudun hijirar wadanda ba daga Karamar Hukumar ta Bama suke ba, da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijirar.

Ya kuma karyata jita-jitar cewa, akwai wata kyauta ta musamman da gwamnatin Jihar ke baiwa wadanda suka koma gidajen na su.

“Muna sane da kokarin da wasu ke yi na lalata wannan shirin na mu, sam wannan maganan ba gaskiya ce ba. Da farko yawan ‘yan gudun hijirar da suka nemi dawowa Bama su 36,000 ne. mun dawo da su ne bisa sharadin nan na Majalisar dinkin Duniya na cewa, duk dan gudun hijirar da zaa  mayar da shi gidansa tilas ne a tanadar masa da matsugunin da ya dace, ruwa da kuma kayan inganta lafiya gami da sauarn kayan bukatar sa na yau da kullum, duk kuma mun yi ma su hakanan din.

 

Exit mobile version