‘Yan Gudun Hijira: Gwamna Gaidam Ya Yaba Wa Hukumar Abinci Ta Duniya

Daga Muhammad Maitela,  Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya yaba da kokarin hukumar bunkasa abinci ta duniya wadda take karkashin lemar majalisar dinkin duniya, dangane da tallafin kayan abinci da take rabawa yan gudun hijira da masu karamin karfi tare da kananan yara jihar; wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu.

Gaidam ya bayyana hakan ne ga Daraktan hukumar a Nijeriya, Madam Myrta Kaulard, wadda ita da tawagar ta suka kawowa gwamnan ziyarar ban-girma jiya da rana a gidan gwamnatin jihar dake Damaturu. Tawagar wadda ta hada da babbar jami’ar hukumar ta jihar Borno, Mista Tito Nikodimos.

Madam Kaulard ta bayyana wa gwamnan cewa ta kawo wannan muhimmiyar ziyarar ne da zimmar gabatar da kanta ga gwamnatin jihar domin neman shawara da tsinkayar wa dangane da fafutukar da hukumar take yi na ganin abinci ya wadatu ga jama’a a yankin arewa maso gabas.

A nashi bangaren, Gaidam ya fara da bayyana godiyar al’ummar jihar Yobe bisa ga ayyukan jinkai da wannan hukumar ga jama’a.

Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana cewa zai yi amfani da wannan damar; ta hanyar wannan ziyarar babbar da Daraktar hukumar WFP tare da tawagar ta, a fadar sa wajen yabo ayyukan jinkai da hukumar ta bayar ga jama’a musamman wadanda suka gamu da ja’ifufin fari, ambaliyar ruwa, hadi da yan gudun hijirar da Boko Haram ta haifar da sauran su a jihar Yobe.

Gwamnan ya ce” a kebance zan kara jaddada yabawa hukumar bisa taimakon da ta baiwa yan gudun hijirar jihar Yobe na kudi kuma hannu-da-hannu ga magidanta sama da 1, 250 a kananan hukumomin Nguru da Gashuwa, kana kuma da karin iyalai 1, 500 wadanda ke jiran a tabbatar musu da irin wannan agajin”.

“Har wala yau dai, irin wannan aikin jinkan hukumar ya gudana ga al’ummar mu masu gudun hijira a kananan hukumomin Gaidam da Yunusari wadanda suka samu iraruwan shuka, tallafin kudi da sauran kayan noma domin gudanar da ayyukan wajen samun wadataccen abinci ga bangaren. Bugu da kari kuma, hukumar ta karfafi yara yan kasa ga shekara biyu sama da 17, 000 da markadaddun kayan abinci, don tunkarar matsalar karancin abinci mai gina jiki da ake fama dashi a jihar”. Ta bakin Gwamnan.

A hannu guda kuma, Gaidam ya yaba wa hukumar dangane da samar da wata cibiya mai koyar da bincike da habaka ayyukan jinkai a jami’ar jihar Yobe. Inda ya ce” kuma ko shakka babu, girka wannan cibiyar zai taimaka gaya wajen dada karsashi da kwarin gwiwa ga ma’aikatan ayyukan jinkai a cikin jihar dama a wajen jihar”. Inji shi.

Wanda a karshe gwamnan ya bukaci wannan hukumar tare da hadin kan majalisar dinkin duniya da su kara kaimi wajen ayyukan agaza wa gwamnatin jihar Yobe dangane da fadi tashin ta wajen ganin ta tallafi kafadun yan gudun hijira a jihar, marasa karfi kana kuma da al’ummar da suka koma muhallan su bayan lafawar wannan matsala ta tsaro wadda ta addabi Yobe da yankin baki daya.

Exit mobile version