Connect with us

JAKAR MAGORI

‘Yan Gudun Hijira Sun Fashe Wa Masari Da Kuka

Published

on

Yayin da Gwamna Aminu Masari da wasu manyan jiga-jigan gwamnati su ka kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira, mata da yara a sansanin da ke yankin karamar Hukumar Faskari a jihar Katsina sun rushe da kuka, kana sun nemi a kawo mu su agaji ta hanyar tallafa mu su sakamakon iftila’in da ya saukar mu su.

’Yan gudun hijirar sun bukaci a samar da zaman lafiya ta yadda za su samu damar koma wa gidajensu. Masari ya ce ya shiga damuwa matuka a kan rashin tsaron jihar tare da tabbatar da cewa za a mayar da hankali wurin komawarsu gida. Suna ta ihun neman taimako tare da tallafi musamman ta bangaren samar da zaman lafiyan da zai sa su koma gidajensu.
Wasu daga cikin matan sun dora hannuwansu a kai yayin da wasu ke faduwa kasa suna kuka. Akwai a kalla mata da kananan yara 3,886 a sansanin. Zaman sansanin ya zame musu dole bayan harin da ‘yan bindiga suka kai musu wanda ya kawo mutuwar da yawa daga cikin su tare da salwantar kadarorinsu.
Ya ce: “Yan bindigar ba su san komai ba da ya wuce karfin bindiga kuma akwai bukatar a yi amfani da hakan wurin maganinsu. Ba za su iya zama daya da dakarun sojinmu ba. “Dole ne jama’a su samar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro don kawo karshen matsalar. Muna rokonku da ku yi hakuri da mu,” a cewarsa.

Advertisement

labarai

%d bloggers like this: