‘Yan Gudun Hijira Sun Tare A Gidan Sarkin Minna

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Kimanin shekaru uku kenan da mutanen kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi suka kasa bacci da idanu biyu a gidajen su sakamakon hare haren mahara a yankunan su wanda zuwa yanzu ya lakume rayuka da dukiyoyi da dama, baya dimbin mutane maza da mata da ‘yan bindigan ke garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Tun da farko gwamnatin Neja ta shelanta daukar matakai tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya da jami’an tsaro. Wanda mutanen da abin ke shafa sun sha bayyana cewar a duk lokacin da suka ji rurin jiragen sama to a ranar ba sa iya bacci domin a irin wannan lokacin ne ‘yan bindigan ke baje hajarsu.
Tun a lokuttan baya akwai ‘yan gudun hijira a cikin garuruwa da ba sa karkashin kulawar gwamnati, wadanda wasu na zaune a gidajen ‘yan uwansu, wasu kuma na zaune a tsofffin kangaye, da wadanda suka watsu cikin garuruwa suna yawon bara ba tare da sanin makomarsu ba.
Mutanen da lamarin ya fi shafa sun hada da yankin karamar hukumar Mariga mai iyaka da Jihohin Kebbi da Zamfara, sai karamar hukumar Rafi mai iyaka da jihar Kaduna da Katsina, sai kananan hukumomin Munya da Shiroro masu iyaka da Jihar Kaduna da karamar hukumar Lapai mai mashiga zuwa jihar Nasarawa da Abuja.
Sakamakon rashin sanin tabbas ga al’ummomin yasa wasu fantsama fadar mai martaba sarkin Minna, inda tilas gwamnati tai masu matsugunni a makarantar faramare ta IBB da ke Minna.
Da daman su musamman mata da yara sun fantsama cikin manyan garuruwa jihar suna yawon barace barace dan samun da zasu ci. Ganin irin wannan halin na ko in kula ya kai ga ‘yan gudun hijira su dubu uku da mafi yawansu mata ne da yara yin sansani gidan mai martaba sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago, wanda ganin hadarin zaman a fadar tasa gwamnatin jiha ta dauki matakin mayar da su farfajiyar makarantar faramare ta IBB da ke Minna.
Da yake bayani ga ‘yan gudun hijirar da suka fantsamo gidan sarkin Minna, gwamnan Neja ya nuna takaicinsa akan yadda lamarin yaki ci, yaki cinyewa. Inda ya cigaba da cewar gwamnati ba za ta zuba ido hakan na cigaba da faruwa ba, domin yanzu hakan an tabbatar min da bullar kungiyar Boko Haram a Kaure cikin karamar hukumar Shiroro tare da kafa tutarsu.
” An tabbatar da alamun bullar kungiyar Boko Haram a yankin Kaure.
” Na ji cewar sun kafa tutarsu a Kaure, wanda ke nuna cewar sun mamaye yankin ke nan, wannan shi ne abinda na ke ta fadawa gwamnatin tarayya a baya ga shi yanzu sun cin ma wannan matsayin wanda ke nuna cewar idan ba a yi hankali ba har Abuja ba za ta tsira ba,” a cewarshi.
Gwamnan wanda ya bayyana matsayin matsalar tsaro a jihar, ya nuna damuwarsa akan halin da mata a yankunan karkarun ke ciki wanda mambobin Boko Haram ke mallake su.
” Sun mamaye yankin, sun kafa tutarsu. An tabbatar min yanzu. Sun karbe matan mutane da karfi,”.
Gwamnan yace ” Boko Haram suna bukatar anfani da wannan yankin a matsayin gidajen su kamar yadda su ka yi a Sambisa”.
Gwamnan yace halin da ake ciki yanzu yana bukatar hadin guiwar masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewar gwamnati ta dauki mataki kuma ba za ta ja baya ba za ta cigaba da yunkurawa sai ta kawo karshen lamarin.
Yace bai cire tsammani ba daga gwamnatin tarayya, ba zai tsaya jira ba, yace lokaci yazo da jami’an soja zasu dauki matakin amshe yankin.
” Ya kara da cewar ban debe tsammani ba daga gwamnatin tarayya kuma ba zan tsaya jiran kowa ba”, a cewarshi.
Bulus Asu wani mazauni Kuchi a karamar hukumar Munya, yace tun watanni uku a baya an daidaita yankin gaba daya.
Asu yace sun shigo jihar nan ne ta iyakar mu da jihar Kaduna ta hanyar Kapana suna garkuwa da mutane suna yiwa mata fyade.
Ya bayyana Kuchi, Guni da Gini, Chiri, Fuka da Kapana da wasu kauyukan suna fuskantar matsalolin garkuwa da jama’a sama da shekaru uku da suka gabata.
Bulus ya yabawa mai martaba sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago na kulawa da ‘yan gudun hijira da ke makarantar faramare ta IBB, inda ya nemi gwamnatin jihar da ta dauki mataki mai tsari wajen kawo karshen yanayin da mutane suka haddasa shi.
………………………..

Exit mobile version