’Yan Jarida Na Da Babban Aiki A Zaben 2019 -Alaramma Tanimu

Fitaccen malamin nan da ke garin Kamfani na gundumar Dutsen – Abba a karamar hukumar Zariya mai suna Alaramma Tanimu Mai Almajirai, ya tunatar da ‘yan jarida da suke Nijeriya babban aikin da ke gabansu na abubuwanda za su faru a tsawon lokutan zabubbukan shekara ta 2019.
Alaramma Tanimu ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya, a tsokacin da ya yi na sabarta – juyartar – siyasa da ke faruwa a lokutan zabe mai zuwa day a shafi rikice – rikicen zabe da in har aka bayyana a kafafen watsa labarai, za a iya samun matsaloli da za su kawo cikas dag a al’umma.
A cewarsa a kawai matsaloli da yawan gaske da wasu baragurbin ‘yan siyasa da babu abin da suka saw a gaba, sai me za su aiwatar, domin kawo hatsaniyar da za ta zama silar tashin – tashina a lokutan zabe.
Alaramma Mai Almajirai ya ci gaba da cewar, ya nunar da cewar, a wannan lokaci ne ya kamata manema labarai su yi taka tsantsan da labarum da za su bayyana wa al’umma, kamar yadda ya ce, in labarum za su kawo rikici, ya dace su tuntubi cibiyoyin da suka dace, domin warware matsalolin da ‘yan jaridar suka gano.
A nan ne ya tabbatar da cewar da cewar, wajibi ne’yan jarida su tsayu ga tsari da kuma dokokin aikin jarida da tsarin aikin ya tanada, domin su bayar da gudunmuwarsu, ta yadda za a fara zaben lafiya, a kuma kammala lafiya.
Da kuma Alaramma Tanimu ya juya ga ‘yan siyasa, sai ya tunatar da su cewar,ya zama wajibi su sanya a zukatansu cewar, Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so ga kuma wanda ya so, Alaramma ya ce, duk dan siyasar day a dauki wannan hanya da fauwala al’amurra ga mai duka, zai sami mulki a cikin sauki, ya yi kuma mutunci a cikin al’ummar da ya ke.
A karshen ganawarsa da wakilinmu Alaramma Tanimu Mai Almajirai ya yi kira ga iyayen yara da su rubanya sa idon da suke yi na yadda suke kula da je – dawon yaransu musamman a lokutanda ake gab da shiga da ya shafi yakin neman zabe da huykumar zabe ta kasa ta tsayar na tsunduma zaben shekara ta 2019.

Exit mobile version