’Yan Jarida Sun Gudanar Da Rangadi Kan Ayyukan Ci Gaban Gwanmnatin Kaduna

Kungiyar ‘Yan jaridu ta Jihar kaduna karkashin jagorancin Kwamared Adamu Yusuf, ta fara wani rangadin zagayen ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar kaduna, karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ta gudanar a daukacin Kananan Hukumomi 23 dake fadin Jihar kaduna.

A yayin da yake jawabi jim kadan da kammala ganin wasu dimbin ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ta gudanar a  ciki da wajen Jihar kaduna, Babban Sakataren Ma’aikatan Ayyuka ta Jihar kaduna, Malam Murtala Dabo, ya bayyana irin dimbin ayyukan ci gaba da wannan gwamnatin ta dauko yi ma Al’ummar wannan jiha, duk da kasancewar gwamnatin na fuskantar barazanar rashin kudadden ci gaba da  gudanar da irin wadannan manyan ayyukan ci gaban Al’umma.

Malam Murtala Dabo, ya kara da cewa daga cikin kudadden da gwamnatin ke tsammanin samu domin karasawa da kuma sabbinta wasu manyan ayyuka da gwamnatin ta dauko, sun hada da bashin Dalar Amurka Miliyan 350 da Gwamnatin Jihar kaduna ta naima daga Babban Bankin Duniya, wanda rashin samun wannan bashi na naiman ya haifarwa ayyukan ci gaban jihar tafiyar Hanwainiya.

Babban Sakataren ya kara da bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna karwashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’I, na da tabbacin cewa za ta samu wannan bashi daga Bankin Duniya duk da tarnaki da wasu Sanatoci suka haifar akan batun, kuma a fili yake babban burin Gwamnatin Jihar Kaduna shi ne, daga martaba da kuma dawo da darajar Jihar Kaduna, yadda zata zama Zakaran gwajin dafi a tsakanin sauran jihohi 36 dake fadin kasar nan.

Gwamnatin Jihar Kaduna dai ta dauko ayyuka na sabunta tituna a dukkanin fadin Kananan hukumomin Jihar 23 dake fadin Jihar kaduna.

Daga cikin wuraren da tawagar kungiyar ‘Yan jaridu ta ziyarta sun hada da Unguwar Tudun Wada, inda Al’ummar Unguwar suka dai shaidawa  Tawagar cewa wannan gadar da suka ziyarta an ginata ne tun zamani Sardauna Firimiyan Arewa,  amma ta karye ba a samu wanda zai Gina ta ba sai a yanzu da Gwamna El-Rufa’i ya kammala aikin baki daya.

Sun kara da bayyana cewa, “Wannan gadar a can baya har akan raba aure saboda babu hanyar da za a wuce idan miji da mata na bangare daban daban shi kenan, amma yanzu kamar an yi ruwa an dauke, Malam Nasiru Tuni ya kammala mana ita wanda dalilin hakan Mayanka dabbobi ta zama kullum sai san barka muke yi.”  Inji jama’ar yankin.

Shi ma a na sa bangaren Sarkin Fawan Kaduna, Alhaji Suleiman Sabo, ya jinjinwa Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i,  sakamakon wannan namijin kokarin da ya aiwatar na wannan makekiyar Gada mai dimbin tarihi da kuma tasiri mai yawa kasancewarta hanya ce ta Mayanka dabbobi.

“Hakika wannan hanya ta hada dimbin al’ummar wannan yankin na Tudun wada da kuma mutanen karamar hukumar Kaduna ta kudu domin suna amfani da ita sosai”. Inji

An dai gina wannan katafaren aikin titi tare da Gada da kuma hanyoyin ruwa mai tsawon mita dari 375 da mita 100 na hanyoyin ruwa, dukkansu an yi aikin ne a kan kudi Naira Miliyan dari da biyar.

Tawagar manema labaran ta Kuma ziyarci wurare irin su Barnawa, Unguwar Rimi, Rafin Guza, Unguwar Sabon kawo, da katafaren titin ‘Yan Majalisu dake Unguwar Dosa, da kuma wurin ajiye manyan motoci na Marabar Jos, da Gwamnatin Jihar kaduna ke gudanarwa.

Exit mobile version