Connect with us

LABARAI

‘Yan Jaridu Sun Yi Zanga-Zanga A Zamfara

Published

on

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Zamfara, watau (NUJ) ta bi umarnin uwar kungiya ta kasa ta gudanar da gagarumar zanga-zanga a kan cin zarafin da jami’an tsaro da ‘yan siyasa ke wa ‘yan jaridun a kasar nan.

Mukaddashin shugaban kungiyar na jihar Zamfara, Kwamared Abubakar Ahmda ne ya jagoranci zanga-zangar da aka gudanar a Sakatariyar kungiyar da ke Gusau Baban burin jihar Zamfara ya. A nan ne ya bayyana cewa’ Suna Allah wadai da yadda ake cin zarafin ‘yan jarida da wulakan ta su a kasar nan.
Kwamared Abubakar Ahmad ya bayyana takaicinsa a matsayinsa ‘yan jaridu masu sadaukarwa da kuma zakulo hanyoyin da za a taimaki al’uma na kuncin rayuwa da kuma kawo wa al’umar dauki

Ya ce duk da kokarin da ‘yan jaridar ke yi kafin buga labarai sai sun tabbatar da gaskiyarsa kuma sun tuntubi masu ruwa da tsaki kan labari, daga jami’an tsaro ne ko kwamnati ko a mutane ne amma, jami’an tsaro ko gwamnati idan abin bai musu dadi ba, sai ya zamo muna cikin barazana da kamu ga jami’an tsaro, su kuma ‘yan siyasa su amfani da ‘yan bangar siyasa wajen cin zarafin ‘yan jaridar.
Kwamaret Abubakar ya kuma kara da cewa ‘yan jaridu abokan kowane ,kuma.sune ke taimakawa wajan Samar da tsaro kuma ke taimakon jami’an tsaro wajan kai dauki ga aluma. kuma ‘yan jaridu sune ginshikin ci gaban siyasa da kuma talata hajarsu yaushe ne za mu makin su ?
Don haka cin zarafin da ake mana ya isa haka,kungiyar mu ta kasa bazata lamunci hakan ba.dan aluma natare da mu kuma sun San mahimmancin mu.
Da yake mikawa Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Alhaji Miranda Sanda  Danjari,takakardar koken Kwamaret Abubakar Ahmad ya bayyana masa cewa wannan Sakone da zai mikawa Gwamna Abdul’aziz Yari,a kan cin zarafin da jami’an tsaro da Siyasa kema ‘yan jaridu don daukar matakin gagawa da kuma wasu korafe-korafen da muke so amagance mana.
Kwamishina Danjari ya bayyana jin dadinsa ga yadda ‘yan jaridun suka gudanar da zanga-zangar cikin al’umana da kwanciyar hankali,Kuma wannan ya tabbatar da cewa ‘yan jarida su ne masu kawo ci gaba da kuma son ci gaban kasar nanyadda ‘yan kungiyar ‘yan jarida ke da karfi, aka ci zarafin ‘ya’yanta su ke bin didigi bisa yadda doka ta tsaro bai kamata ba a ce ‘jami’an tsaro da ‘yan siyasa na cikin zarafin su dan cigaban tsaro da siyasa bai tabbatar sai da gudummuwar ‘yan jarida.
Kwamishinan ya dau alwashi mika wa kwamna Abdul’aziz Yari Sakon ‘yan jaridar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: