Connect with us

LABARAI

’Yan Jaridun ‘WASH MEDIA NETWORK’ Sun Fara Aikin Wayar Da Kai Game Da Ingancin Muhalli

Published

on

A ci gaba da kokarin kungiyoyi masu zaman kan su a Nijeriya wajen inganta harkar rowan shad a muhalli kungiyar Water Aid mai rajin samar da tsabtataccen ruwan sha da inganta muhalli ta nemi taimakon ‘yan jarida game da wayar da kan jama’a musamman mazauna karkara domin inganta tsabtar muhalli da ruwan sha saboda a samu ingancin kiwon lafiya da kuma rage yaduwar cututtukan da ake samu ta hanyar gurbataccen ruwan sha ko rashin ingantaccen muhalli.

A yayin wani taro da ta gudanar da manema labarai kungiyar ‘yan jaridu mai ruhoto kan lamurran da suka shafi tsabtar ruwa da muhalli wato Wash Media Network ita ne ta yi wannan kira  a masaukin baki na Command Guest da ke Bauchi, inda suka ja hankalin kafofin watsa

labarai  jaridu da talabijin da rediyo da su himmatu wajen wayar da kan mutane da gwamnati don a samar da ci gaba a fannin tsabtar mushalli da kuma samar da ruwan sha wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar mutane.

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun ta Wash Media Network Mista Wale Elekolusi shi ne ya yi wannana kira lokacin da ya ke ganawa da ‘yan jarida masu ruwa da tsaki kan aikin wayar da kan jama’a game da inganta ruwan sha da tsabtar muhalli a Jihar Bauchi. Inda cikin jawabansa ya bayyana cewa wannan kungiya tana aiki da ‘yan jaridun Radiyo da talabijin da jaridun takardu don isar da sakon wayar da kan jama’a musamman mazauna yankunan karkara game da tsabtar ruwa da muhalli. Ya ce kungiyar Water Aid mai zaman kanta wacce ke samun tallafin wasu kasashe a duniya ita ne ta yi musu rijista da gwamnati don a kara yawan ilmantar da jama’a da ke jihohi takwas da da kungiyar ke aiki a cikin su wadanda suka kunshi Filato da Binuwai da Ekiti da Lagos da Bauchi da Abuja da Enugu da Jigawa yadda a kowace Jiha akwai wannan kungiya.

Kadan daga cikin ayyukan kungiyar ta wayar da kai shi ne halartar tarukan tsabtar muhalli na karshen wata da yin bitar halin da ake ciki game da tsabtar ruwa da muhalli tare da lura da irin taimakon da gwamnati ke yi da kuma irin kuskuren da mutane ke yi game da wannan aiki.  A saboda haka suke shirya taron bita ga ‘yan jaridu kamar yadda tsarin mulkin su ya tanada don a kara zaburar da su game da yadda za su rika bin diddigin labaran da suka shafi tsabtar muhalli da samar da ruwan sha mai kyau.

Wale Elekolusi ya kara da cewa kungiyar Water Aid ta fara aiki a shekarar 1996 kan wannan manufa  kuma Jihar Bauchi na cikin manyan wuraren da suke gudanar da aiki wa mutane yadda suke gudanar da wani babban aiki da tallafin bankunan  kasar Hong Kong da Shangai China suke daukar nauyi, don haka ake da bukatar inganta wayar da kan jama’a game da wanka da wanki da wanke hannu da tsabtace muhalli tare da tabbatar da an samu ruwan sha mai tsabta a dukkan kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi, saboda a tabbatar da cewa kashi 33 cikin dari na cututtukan da ake samu suna samo asali ne daga ruwan sha ko a sakamakon rashin magewayi mai kyau yadda mutane ke bayan gida barkate wanda ke zama musabbabin watsuwar kwayoyin cuta a ciki da wajen muhallan su.

Don haka yana daga cikin aikin wannan kungiya wayar da kan mutane ta kafafen labarai don su dauki gina magewayi da muhimmanci saboda shi ne zai taimaki kowa ya ji dadin muhallin da ya ke zaune a ciki, tare kuma da samar da hanyar samun ruwan sha mai tsabta don amfanin yau da kullum. Yadda ya bayar da misali ga ko bakunta mutum ya je idan an bashi daki abu na gaba da zai nema shi ne magewayi saboda muhimmancin sa ga dan adam. Don haka wannan kungiya ta Water Aid ke kashe mukudan daloli don gina magewayi a cikin garuruwa da makarantu ko kasuwanni da tashoshin mota, saboda a kare yaduwar cututtuka irin su kwalara da maleriya wadanda tushen su shi ne rashin ruwan sha mai tsabta ko rashin tsabtar muhalli

Don haka ya ce kafafen labarai suna da muhimmanci wajen dagawa da nakasawa saboda haka suke son a tallafa don gwamnati ta ji manufar su kan wannan aiki don a ceci rayuwar mutane. Inda ya kara da cewa  suna fiskantar matsala idan sun nemi tallafin hadin guiwa da gwamnati ko neman goyon baya game da gudanar da ayyuka amma akan yi dogon turanci da bata lokaci kan abubuwa masu muhimmanci da suke bukatar gaggawa domin amfanin mutane. Don haka ya kwadaitar da mutane da su rika aika koken su akai akai ga gwamnati don ta inganta musu muhalli da samar da ruwan sha, hakan shi ne zai taimaka su samu ci gaba a wannan aiki cikin gaggawa don a kare rayukan mutane daga kamuwa da irin wadannan cututtuka da idan an je asibiti sune suka fi kashewa da wahalar da mutane irin su maleriya da bakon
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: