Daga Muhammad Maitela,
Rundunar `yan sanda a jihar Yobe ta bayyana cewa a halin yanzu sun yi rajistar sama da mutum 2,000 wadanda suka yo kaura zuwa jihar Yobe, tare da kira ga al’umma su ci gaba da sa ido dangane da yadda jama’a ke shigowa jihar daga garuruwan Gubio, Magumeri, Kaga da Kunduga na jihar Borno.
Rundunar ta sanar da hakan a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun jami’inta na hulda da jama’a ASP Dungus Abdulkarim, a birnin Damaturu, ranar Alhamis.
Abdulkarim ya sanar da cewa, ga dukan alamu al’ummar sun kauro ne daga yankunan su na asali saboda yanayin matsalar tsaron da ta addabi garuruwan su.
Har ila yau, ya bayyana cewa mafi akasarin mutanen suna garuruwan Geidam, Tarmuwa, Gujba, Kuka Reta hadi da kauyukan Kasesa da Kalallawa da ke kusa da Damaturu.
A hannu guda kuma, Kakakin `yan sandan jihar Yobe, ta bayyana cewa haduran motoci sun ci rayukan mutane kimanin 147 a hanyoyin daban-daban a fadin jihar, a cikin shekarar 2020, a sanarwar da ta fitar ranar Alhamis.
Ya fara da bayyana cewa, “A kididdigar da muka gudanar ya nuna sama da haduran mota 200 ne suka faru a jihar, ta hanyar alkaluman da sashen kula da hadura na rundunar (Traffic Department) ya fitar; daga 1 ga watan Janairun 2020 zuwa yau.”
“A wadannan haduran mota 41, wanda hakan ya yi sakamakon mutuwar mutum 147 karin wasu da dama kuma sun samu raunuka.”
“Bugu da kari kuma, bincike ya nuna yadda gudun ganganci, tuki ba bisa ka’ida tare da taka dokokin tuki ne su ka yi ummul-haba’isan yawaitar haduran.”
Haka zalika kuma, Kakakin Rundunar `yan sandan, ya bukaci direbobi da duk masu ruwa da tsaki a fannin da cewa su rinka taka-tsan-tsan da kiyaye dokoki a lokacin tukin, tare da jan kunne ga duk wanda aka kama da take doka, zai dan-dana kudarsa.