Kimanin ‘yan kallon kwallon kafa 10,000 za su koma shiga filin wasa domin kallo daga tsakiyar watan Mayu a shirin da gwamnatin Ingila ke yi na kawo karshen dokar kulle a wani jawabi da gwamnatin kasar tayi a ranar Litinin.
Firai Minista, Boris Johnson ya sanar da matakai hudu da aka tsara domin janye dokar killace kai don gudun yada cutar korona sannan za a koma yin wasannin da suka hada da na kwallon kafa da kwallon golf da na tennis daga 29 ga watan Maris.
Za kuma a cimma hakan ne idan har aka samu nasara kan allurar riga kafin annobar da tasirinta kafin a amince a dage dokar kullen gabaki daya a cewar Fira Ministan, wanda shima cutar ta taba kamashi a shekarar data gabata.
Za a bude wuraren shakatawa da na motsa jiki a rufaffen wuri da wuraren linkaya daga ranar 12 ga watan Afirilu sai dai ana ci gaba da gudanar da gasar Premier League ba tare da ‘yan kallo ba, sannan kuma ana yi wa ‘yan wasa gwaji a kowanne mako.
Amma daman tuni kungiyoyin kasar ta Ingila musamman wadanda suke buga gasar firimiya suka fara kira ga hukumomi a kasar dasu bayar da damar magoya baya su fara shiga fili domin samun kudaden shiga bayan da tattalin arzikin kungiyoyin gaba daya ya karye sakamakon annobar cutar Korona wadda ta dakatar da komai.
Kungiyoyi da dama dai sun karye sakamakon kamuwa da cutar Korona wanda hakan ya shafi kokarin manyan kungiyoyi kuma sannan yasa ba’a kashe kudi ba a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa guda biyu da aka bude a baya.