Mustapha Ibrahim" />

‘Yan Karota Sunyi Batan Dabo A Titinan Birnin Kano

Duk da yadda jamian hukumar kula da ababen hawa da hana cunkoso a Jihar Kano, wacce a ka fi sani da Karota, su ka saba bayar da gudunmawa a kowace rana kan manyan titinan birnin Kano, domin tabbatar da dokar tuki da hana ganganci, amma a jiya Lahadi an wayi gari babu jamian na Karato ko daya a kan titi, inda kuma jamaa da dama su ka yi mamaki da alajabi na batan dabo ko kusufi da ’yan Karotan su ka yi a birnin.

Rashin ganin ’yan Karota a kan hayoyin Kano ya ba wa mutane da dama mamaki, musamman a daidai lokacin da shugaban hukumar, Baffa Babba dan Agundi, ya yi barazana da kurarin sa kafar wando daya da duk wani mai mashin da ya yi goyo bisa dogaro da dokar hana acaba ko kabu-kabu ko okada a Kano, amma sai a ka wayi gari babu jami’in Karota a Gabas da Yamma, Kudu da Arewa na titinin Kano a jiya.
Hakan ya jawo bayanai daban-daban daga bakunan mutane na cewa sun samu matsala ne da jamian tsaro har ma an kama wasu da dai sauran bayanai da matane Kano su ka rika furtawa na rashin ganin su a wannan rana kodayake wasu rahotanni sun bayyana cewa akwai wata kungiya mai Alaka da kare hakkin biladama da kuma tabbatar da doka da oda ta yi barazanar  daukar matakin sharia kan hukumar Karota bisa zargin da a ke yi ma ta na wuce gona da iri da kuma yin aikin doka ba tare da damar yi ba a dokance.
Sai dai bayan zagayen gani da ido da Wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi a manya da kananan titinan birnin Kano daga Asibitin Murtala zuwa Na’ibawa Bypass, daga Gidan Murtala zuwa Titin BUK, Ibrahim Taiwo Road zuwa Mariri da dai sauran muhimman titina bai ga jami
in Karota ko daya ba a wannan Rana, sai ya tuntubi kakakin Hukumar Karota, Malam Nabilisi Kofar Naisa, ta wayar hannu, inda ya ce, kodayake mutane su na ta yada jita-jita a kan wannan lamari, amma dai shi a iya saninsa babu wani abu sabo da ya sani, illa a ganinsa bai wuce wannan rana ce ta Lahadi  ba, kuma an samu ruwan shuka, kuma wasu jamian Karato daga kauyuka su ke zuwa. Don haka su ka tsaya su yi shuka, kuma ya na tunanin wannan wani gwaji ne na a ga ko komai zai iya tafiya daidai a ranar Lahadi ba tare da jamian Karota ba a Kano, saboda kasancewar rana ce da ba a yin kullen Korona a jihar.
Ya ,ce wannan shi ne tunaninsa, amma tunda bai zauna da shugabannin hukumar ba, ba zai ce komai ba a hukumance tukunna.
To, amma dai wata majiya ta shaida ma na cewa, yin batan dabon ’yan Karotar watakila ba zai rasa nasaba da wani sabani da ya shiga tsakaninsu da jami’an tsaro ba, inda a ka yi mu su kashedin fitowa bakin aiki, saboda zargin wuce gona da iri da a ke yi mu su.

Exit mobile version