Ibrahim Ibrahim" />

’Yan Kasuwa Ku Sassauta Sai Allah Ya Sassauta Mu Ku – Na’ibi Sulaiman

An bayyana Watan Ramadan a matsayin wata babbar baiwa da Allah (SWT) ya yi wa al’ummar Musulmi da ita, kuma dukkanin wani mutum Musulmi da Allah ya tsawaita rayuwarsa zuwa Watan Ramadan to shakka babu Allah ya yi masa wata gagarumar baiwa wacce wasu jama’a da dama basu samu irin ta ba.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani Malamin Addinin Musulunci mazaunin Garin Kaduna, wanda kuma shi ne babban limamin Masallacin Darul Kur’an, dake Kaduna, Malam Naibi Sulaiman Musa, a yayin da yake gabatar da tafsirin watan Azumin Ramadan, wanda ya saba gabatarwa a kowa ne shakara.
Malam Naibi Sulaiman, ya ci gaba da cewar, hakika Allah ya zabi Watan Ramadan akan sauran Watannin Musulunci 11, domin a cikin watan ne aka saukar da Alkur’ani mai girma, sannan dukkanin wani aikin Alkhairi da Mutum ya yi a cikin Watan Ramadan, Allah yana ribanya shi ninkin ba ninkin, sannan a cikin wannan wata ne Allah ya samar da wani Dare mai suna Daren Lailatul Kadari, wanda wannan dare daya yana matsayin Watanni dubu ne, wato idan aka dauki lissafi Daren Lailatul Kadari na matsayin shekaru 84 ne, lallai wannan ba karamar baiwa ba ce, a cewarsa.
Malamin ya ci gaba da cewa, ya inganta a hadisi Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewar Mala’ika Jibirilu, ya yi Addu’a sannan ya bukace shi da yace Amin, Addu’ar kuma ita ce, Allah ya la’anci wanda duk ya riski Watan Ramadan sannan ya gagara yin aikin da Allah zai gafarta mishi a ciki, sannan Annabi ya ce amin, dalilin wannan la’anta kuwa shi ne, irin garbasa da ke cikin Watan Ramadan amma ace Mutum ya kasa aiwatar da aikin da zai samu gafara a ciki, babu shakka wannan Mutumin ya tabe.
Saboda haka ya bukaci Jama’ar Musulmi da kada su yi sake da wannan dama da Allah ya basu, su dage wajen yawaita Istigifari da karatun Alkur’ani da yawaita Sadaka da Nafiloli domin dacewa da samun garabasa da ke cikin wannan wata.
Malam Naibi Sulaiman, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa Musulmi da cewa, su ji tsoron Allah Ubangijinsu kada su kara tsawwala farashin kayayyakinsu da nufin cin kazamar riba a cikin Watan Ramadan, ya kamata ‘yan kasuwarmu su gane Watan Ramadan wata ne na neman Lada da dacewa a Lahira, ba wata ba ne na tara abin duniya ba, kamata ya yi a ce cikin Watan Ramadan Jama’ar Musulmi harma da wadanda ba Musulmi ba, sun sami sauki ta fuskar kayayyakin masarufi, domin a wasu kasashe da suka ci gaba na Musulmi ana zabtare farashin kayayyakin masarufi domin su samu sauki a cikin watan, sannan su kansu ‘yan kasuwan su dace da samun gagarumar lada a wajen Ubangijin su.
Dangane da batun Malamai masu gabatar da Tafsiri a lokacin Watan Ramadan kuwa, Malamin ya janyo hankalinsu tare da kira a garesu da yin koyi da tsarin gudanar da tafsiri irin yadda sanannen Malamin Addinin Musulunci nan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya gudanar, wato gabatar da Tafsiri cikin tsantseni da Ikhlasi, ba tare da kaucewa ainihin tsarin tafsirin ba, wanda wannan shi ne dalilin da yasa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, ya jima da rasuwa amma har yanzu karatun shi ke da tasiri matuka. Saboda haka, ya na kira ga Malamai masu gabatar da tafsiri a wannan wata na Ramadan, su tsaya akan karantawa bisa ga tsari na Kitabu Was Sunnah, domin neman yarda a wajen Allah (SWA) da kuma dacewa da samun rahama a ranar gobe Kiyama. A cewarsa.

Exit mobile version