Daga Ibrahim Muhammad, Kano
’Yan kasuwa a Kano na shirin shiga a dama da su wajen neman takarar Gwamnan jihar Kano don magance watsi da ake yi da bukatunsu da zarar sun dafa wa ’yan siyasa sun kai ga gaci.
Sun yi korafin cewa sau da dama sukan tura mota a madafun siyasa daban-daban, amma abin takaici, da motar ta tashi sai a bulbule su da hayaki a gudu,ko sauraronsu ba a yi duk kuwa da dinbin matsaloli da suka dabaibaye harkokinsu.
A maimakon haka, sai sun tallafa an kafa gwamnati, sai a nemi a kassarasu, ta kassara harkokin kasuwancinsu, ta jibga musu dinbin karin matsaloli maimakon a warware musu, da yi musu katsalandan a harkokin kungiyoyinsu.
‘Yan kasuwar da dama sun yi nuni da cewa suna da duk wata dama da za su shiga a dama da su a harkokin siyasa, domin,su suke bada gudummuwa mafi yawa da dukiyoyinsu da kuri’unsu wajen kaiwa ga nasarar zabar gwamnati.
Saboda haka yanzu lokaci ya yi da su ma ya kamata su nemi takarar kowace irin kujera ta mulki a kkasar nan, tun, daga kan shugaban kasa har Gwamna.
Wani daga ‘yan kasuwar, Malam Iliyasu Koki ya shaida wa manema labarai cewa dukkan shugabanci a fagen siyasar kasar nan sai da yawun ‘yan kasuwa. Dan haka ya yi kira ga ‘yan kasuwa su hada kai don ciyar da kasuwanci gaba, ta tsaida ‘yan takara na Gwamna da majalisun jiha da na tarayya da Sanatoci.
Shi ma a nasa bangaren, wani dan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru mai Sabulu da ke Kasuwar Kwanar Singa, wanda a baya ma ya taba yin kira ga shahararen dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote ya fito neman takarar shugabancin kasar nan. Ya ce, ‘yan kasuwa na iya juya akalar siyasar kasar nan.
Kabiru Mai Sabulu,wanda yake a matsayin Jakadan zaman lafiya na majalisar Dinkin Duniya, ya kafa misali da shugaban kasar Amurka, Donald Trumph da cewa dan kasuwa ne kafin ya zama shugaban Amurka. A nan kusa kuma ga Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, wanda shi ma dan kasuwane.
Abubuwa masu Kyau na dimokaradiya shine kowa na da damar neman duk abin da yake sha’awa.
Yace Jam’iyar APC na da matakai daban daban na gudanar da abubuwan ta, inda yace reshen Jam’iyar na jihar zai gabatar da bukatan yan mazabar arewacin jihar na samun kujerar takarrar Jam’iyar ta gwamna ga duk wadanda suke da haki domin jin nasu ra’ayoyin su kafin a kai ga cimma matsayin karshe.