Hakika ‘yan kasuwar jihar Kano dana sauran kasuwannin da ke kasar nan suna taimakawa gwamnati wajen samar da aikin yi ga al’umma musamman matasa maza da mata ga wadanda suka kammala karatun su dama wadanda ba su yi ba.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin manajan daraktan sayar da yadi na SAHAL dake kan hanyar zuwa IBB a Kano, Alhaji Ibrahim Ado Abdullahi, a lokacin da ya ke tsokaci game da yadda ‘yan kasuwa a kasar nan ke taimakawa gwamnati wajen samar da aikin yi ga al’umma.
Malam Ibrahim Abdullahi, ya ba da misali da yadda wasu ‘yan kasuwar da suke da manyan kantuna ke daukar ma’aikata masu yawan gaske, wanda hakan zai rage zama kawai da suke yi agida ba bu aikin yi, sannan kuma za su koyi yadda ake kasuwanci musamman idan sun mayar da hankalin su.
Har ila yau inji manajan daraktan na SAHAL wani abu kuma muhimmi shi ne yadda ‘yan kasuwar ke habaka tattalin arzikin jihohi da kasa baki daya, ba ya ga samar da kudaden shiga ga gwamnati. Ya tabbatar wa da manema labaran cewa akwai akalla mutane kimanin 50 da ya dauke su aiki yanzu haka a SAHAL, abin sha’awa yawancin su duk suna da ilimin zamanin zamani dana addinin musulunci.
Alhaji Ibrahim Ado Abdullahi, ya roki gwamnati da ta mayar da hankali akan samar da hasken wutan lantarki ta yadda za’a samu gudanuwar al’amura cikin sauki da kwanciyar hankali.
Ya nuna alhinin shi game da yadda masu garkuwar da mutane domin karbar kudin fansa suka yi garkuwar da wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin kwari akan hanyar su ta zuwa garin Aba domin huldar kasuwanci wannan abin bakin ciki ne sosai saboda haka yakamata gwamnati ta kara kaimi akan samar da tsaro.