‘Yan Kasuwa Su Shiga Tsarin Inshorar Musulunci

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran masu sana’o’i  da manoma su rungumi tsarin Inshorar Takaful da Ja’iz ta ƙaddamar a jihar.

Akanta Janar ta Jihar Hajiya Aisha Muhammad Bello ta bayyana hakan a lokacin da ta wakilci Gwamna Ganduje a wajen kaddamarda Inshorar a Kano.

Ta ce, yan kano yan kasuwane da masu sana’o’i tsarin InshorarTakaful tsarine na taimakekeniya, kowa ya san a rayuwa akwai riba akwai kuma asara, wannan mataki ne na yin rigakafi ga duk wata ƙaddara ta hasara da ka iya samun mutum wanda hakan kuma bai saɓawa tsarin musulunci ba.

Hajiya Aisha Muhammad Bello ta gode wa Sarkin Kano, Malam Muhammad Sunusi bisa goyon bayan da ya bai wa wannan tsare-tsare don ganin ya tabbata saboda irin goyon baya da ya bayar lokacin yana gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN). Ta ce gudummawar ta Sarkin Kano Sunusi ta haifar da samun wannan inshora da makamantansu.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sunusi na biyu ya ce, kullum ana fuskantar asara ta ɓangarori daban-daban ta gobara ko hatsari ko sata amma mutum ba shi da yadda zai yi ya maida asara.

Ya ce, akwai buƙatar ta maye gurbin asara ta ɗaukar nauyin juna ta tsarin Inshorar takaful, wanda tsari ne na jama’a su haɗu su riƙa sanya wani abu a asusu da yardar cewa in wani ya sami asara a taimaka masa ya maida asarar da yayi.

Sarkin na Kano Muhammadu Sunusi ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta yi wa dukkan motocinta da gine-ginenta wannan inshora.Ya ce, su ma a fada zasu yi ƙoƙarin ganin duk motoci mallakar masarautar Kano sun samu yin inshorar takaful.

Da yake jawabin maraba, shugaban Bankin Ja’iz, wanda kuma shi ne ya samar da Kamfanin na Ja’iz takaful inshora Alhaji Dakta Umar Abdulmutallab ya ce, Sarkin Kano Muhammad Sunusi ya yi rawar gani wajen kafa bankin Ja’iz, wanda ta silarsa ne aka kafa inshorar takaful. An kafa takaful ne don kafa inshorar musulunci don tabbatar da cewa mutane sun azurta ta halal.

Dakta Umar Abdulmutallab ya ce, kano ce ta zama jihar farko da suka ƙaddamar da kamfanin. Ya yi kira ga jama’a da su bada haɗin kai don cimma gajiyar tsarin na inshorar musulunci.

 

Exit mobile version