’Yan kasuwan mai sun bayyana cewa, a shirye suke su gyara matatun man Nijeriya wadanda suka kwashe shekara da shekaru ba sa aiki, sanna za su zuba kayyayakin aiki wanda cikin karamin lokaci za su farfado. Bangaren ‘yan kasuwan da suke sarar man daga wajen sari su suka bukaci gwamnatin tarayya da su bari ‘yan kasuwa su ja ragamar matatun mai na kasar nan. An bayyana cewa, ‘yan kasuwan man su taka mahimmiyar rawa wajen tara kudade domin a samu damar farfado da matatun man kasar nan.
Matatunn mai na Nijeriya sun hada da na Kaduna da Fatakwal da Warri sun dauki tsawan shekara da shekaru da su tace danyan mai ba duk da irin kudaden da kamfanin mai na kasa (NNPC) yake kashewa a kan matatun. An dai fitar da wani rahoto a ranar 23 ga watan Nuwamna wanda ke nuna yawan kudade da aka kashe wa matatun, wanda ya kai na naira biliyan 81.41 tun daga watan Junairu har zuwa watan Agustan wannan shekara, amma har zuwa wannan lokaci matatun man ba su tace mai ko digo ba.
Domin magance wannan lamari, ‘yan kasuwan man sun bayyana wa manema labarai a Abuja cewa, suna da damar da za su iya gyara matatun man tare da gudanar da kasuwancin hadin gwiwa idan suka sami nasarar gyarawa.
“Ya kamata gwamnati ta kira ‘yan kasuwa ta mika musu jan ragamar matatan mai daya ko biyu tare da gudanar da kasuwancin hadin gwiwa domin matatun man su ci gaba da aiki yadda ya kamata,” in ji shugaban kungiyar ‘yan kasuwan man ta kasa, Billy Gillis-Harry.
“Ya kamata mun dauki hanyar yadda za mu gyara farashin mai da kanmu, idan har matatun man mu suna aiki yadda ya kamata, to za a sami saukin farashin mai a cikin kasar nan.
“Ya kamata a bai wa ‘yan kasuwa damar gudanar da matatan mai daya ko biyu, saboda muna da damar gyara matatunmu su ci gaba da aiki yadda ya kamata.
“A shirye muke mu hada kai da gwamnati da kamfanin NNPC wajen gudanar da kasuwancin matatun mai domin samun riba wanda za a raba a tsakanin mu.”
Ya kara da cewa, dukkan ‘yan kasuwan man da ke cikin kasar nan abin da suke bukata bai wuce son gudanar ganin an gyara matatun mai ta yadda za su dunga aiki domin a samu saukin farashin mai a Nijeriya.
Gillis-Harry ya ce, “muna bukatar a ba mu matatun mai na Warri da na Fatakwal domin mu hada kai da gwamnati wajen farfado da matatun ta yadda za mu sami damar kayyade farashin mai da kanmu.”
Ya ce, ‘yan kasuwan mai a shirye suke su saya wa gwamnati kayayyakin da take bukata domin gyara matatun man.
“Idan gwamnati ta ba mu damar mu saya za mu yi farin ciki wajen samo kudade, saboda za mu gudanar da kasuwancin hadin gwiwa a ko’ina a fadin duniya domin tabbatar da cewa tattalin arzikin kasarmu yana aiki yadda ya kamata,” in ji shugaban ‘yan kasuwan man Nijeriya.
“Saboda kowani lita daya na mai da aka siya ana danganta shi ne da dalar Amurka, sannan ba mu gudanar da tattalin arzikinmu da dala, muna gudanarwa ne da naira.
“Muna shigowa da kudaden kasashen waje a ko da yaushe a cikin harkokin tattalin arzikinmu, wannan shi ne ya hana tattalin arzikinmu ci gaba.
“Wannan ne dalilin da ya sa ‘yan kasuwan mai ke bukatar gwamnati ta ba su damar gudanar da harkokin matatun mai saboda su ci gaba da aiki yadda ya dace.”
Lokacin da aka tambaye shi ko rage farashin mai da aka yi na naira biyar zai kara kawo tallafin, Gillis-Harry ya bayyana cewa ba zai kawo ba. Ya tabbatar da cewa, zamanin bayar da tallafi ya shude wanda ya sa abubuwa suka tsaya a haka. Ya kara da cewa, idan gwamnati ta dawo da bayar da tallafi, to shi zai kayyade yanayin irin tattalin arziki a cikin kasar nan.