Daga Yusuf Abdullahi Yakasai,
Hadin kai shi wani babban al’amari ne da, idan babu shi ba wata maganar cigaban da za a yi. Don haka akwa bukatar ‘yan kasuwanmu na arewa da ke sana’a a Legas mu hada kai don samun cigaba.
Daya daga cikin ‘yan kasuwan arewa mazauna Legas, Alhaji Muhammadu Alaba ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Legas, inda kuma ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda wasu ‘yan-kasuwa suke ta fadace fadace a tsakaninsu, saboda neman shugabanci.
Ya yi kira da su kar fa su manta, sun zone domin neman alheri, ba wai sun zo Legas bane don (fadace – fadace), ya ce “Kada mubar wa ‘ya’yanmu abin kunya, a wurin da muke neman”. Abincin mu ya kamata mu tuna daga inda muka fito.
Daga karshe ya ja hankalin matasan dasu tashi tsaye wajen neman sana’a, ya kuma roki su iyayen kasuwar dasu dubi Allah su bada shawara wadda take ta gaskiya, kada su bi son zuciyarsu, wannan ita ce manufar.
Ya kuma godewa su ‘yankasuwa maza da mata, cewar a kara hakuri da juna Allah ya taimakawa kowa. Ya kuma jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda kokarin da yake yi wajen samar da wanzuwar zaman lafiya, abinda kuma ya ce wannan shi ne addu’ar su koyaushe.