Connect with us

KASUWANCI

’Yan Kasuwan Nijeriya Sun Nemi Tallafin ECOWAS Kan Tsangwama Daga Ghana

Published

on

Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta ‘Yan Najeriya sun hallara a Sakakaraiyar Skatariyar ECOWAS dakz birnin tarayyara Abuja don gusanar da zanga-zangar lumana akan zargin da suka yi na cewar ta kawo masu wauki saboda kulle masu shagunansu da ake yi a ksar Ghana.

‘Yan Kasuwar sun gudanar da zanga-zangar ce a ranar litinin data wuce da karfe 9:30 na safiyar ranar, inda ayyuka suka tsaya chak a Sakatariyar ta ECOWAS. Sun gudanar da yin tattaki akan titunan Yakubu Gowon dake anguwar  Asokoro, inda hakan ya janyo aka samu yin chunkoson ababen hawa. ‘Yan kasuwar sun fito ne suna dauke da Allunan da suka yiwa rubutu irir-iri kamar haka,”muna bukatar ECOWAS ta kawo mana dauki, Ghana ta sake bude mana shagunan mu a cikin gaggawa, bazamu taba lamunta da lamarin dake aukuwa a Ghana ba da sauransu. A jawabinsa a lokacin zanga-zangar Shugaban kungiyar Ken Ukaoha yace, kungiyara ta yi zanga-zangarce sabida da yadda ake cin zarafin ‘yayanta a Ghana, inda ya yi nuni da cewar lamarin ya kazanta domin ‘yan Majalisar kasar sun gabatar da dokar data ke bukatar kawo rudu ga wadanda ba ‘yan kasar ba da suka zuba jarinsu a kasar ta Ghana. Ukaoha ya yi nuni da cewar, tunda kasar Ghana ta na daya daga cikin ‘yayan ECOWAS, akan shigar da kaya ba tare da wata tsangwama ba akwai bukatar ECOWAS ta ta gargadi gwamnatin  kasar ta Ghana akan lamarin. Har ila yau, kungiyar ta bawa ECOWAS wa’adin sati daya data kawo dauki akan lamarin, in kuma har bata yi wani abu akai ba, zata tattaro kan daukacin  ‘yayan ta don suyi zaman dirshan a harabar Sakatariyar ta ECOWAS. Ukaoha yaci gaba da cewar,tuni kungiyar ta rubata takardar koke zuwa ga Shugaban ECOWAS Jean-Claude Brou, da Shugaban kasa  Muhammadu Buhari akan lamarin. Takardar koken wadda kungiyar ta bawa wakilin lu kwafi, tana dauke da kanan wata 24 ga watan Satumbar 2018. Koken shine kamar haka,” muna bukatar a kawo mana dauki a cikin gaggawa kuma munyi zanga-zangar ce don mu sknar da kai akan jin tsoron da luke yi, tsangwamar da ake nuna mana da kuma rashin tsaro da aka jefa ‘yan kasuwar ‘yan Najeriya dake Ghana da gwamnatin ta kasar ta bari ake yi masu da kuma ‘wasu ‘yan kasar dake sassa da ban-da- ban na kasar da cibiyar zuba jari ta kasar ta kitsa da kuma Ma’aikatar kasuwanci da Masana’antu.” Yace,” mun rubuta zuwa gare ka don sanar da kai akan lamarin kuma kai maganar zuwa ga hukumar a lokuta fa dama akan lamarin akan sanatwar da Ma’aikatar kasuwanci da Masana’antu ta fitar akan wa”adin da aka bawa ‘yan kasuwar da ba ‘yan kasar bane  a ranar 27 ga wktan Yuli na 2018 na su fice daga kasuwannin.” Shugaban yaci gaba da cewar,a cikin watan Agustan 2018 Ma’aikatar kasuwanci da Masana’antu da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ra kasar sun gabatar da fatirol na musamman don aukuwa ‘yan kasuwa ‘yan Najeriya dake Ghana, inda hakan ya janyo aka kulle masu shaguna 400/a garin Kumasi da Ashanti.” A karshe Shugaban yace,” an rufewa “yayan kungiyar mu harabar  kasuwancin su da basu umarnin su tashi a ranar  27, ga watan Yulin  2018, inda suka bukaci sai mun biya dala miliyan daya na harajin zuba jari a kasar.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: