Daga Yusuf Abdullahi Yakasai,
Alhaji Sa’adu Gulma jawabinsa lokacin da aka yi babban taro na kaddamar da Shugabannin kasuwar ta Ijako, a matsayinsa na uban taro,ya godewa kabiyesi da Bale, da suke shugabanci a wannan Gari. Alhaji Sa’adu Yusuf Gulma hakika ya bayyana farin cikinsa cewa, akwai zaman lafiya tsakanin su, kuma wannan kasuwa a shirye suke da su kare mutuncin kowa.
Bugu da kari ya yi roko ga jama’a kan muhimmancin zaman lafiya a wannan gari Ijako. A matsanyisa na daya daga cikin manyan ‘yan kasuwar, ya nuna farin cikin ganin yadda ‘yan kasuwar suke gabarta kasuwancinsu. Wanda kuma a cikin farin ciki da walwala. Daga karshe Alhaja Sa’adu Yusuf Gulma ya taya sababbin Shugabannin murna da farin ciki Allah ya taya su riko.