Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Wasu yan kunar bakin-wake guda uku; biyu maza daya ta mace, wadanda ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun tayar da bama-baman dake jikin su inda sama da mutane 13 suka rasa rayukan su, a kauyen Mashimari na yankin karamar hukumar Konduga, a jihar Borno.
Wata majiya ta kut-da-kut daga yan sintirin kato-da-gora a jihar Borno ta shaidawa wakilin mu ta wayar tafi-da-gidan ka cewar yan kunar bakin-waken tada bama-baman dake jikin su ne jim kadan bayan karar harbin iskar da jama’ar kauyen suka ji, a kokarin su na kubuta da rayukan su.
Bayanan sun tabbatar da cewa harin ya faru ne a kusa da matsugunin yan gudun hijirar Mandarari, wanda aka kaiwa hari a cikin watan August, kwanan baya. Tare da bayyana cewa”da farko Boko Haram sun fara da bude wuta da kimanin karfe na safiya ranar litinin, a daidai lokacin da mazauna wannan kauyen ke kokarin gudu zuwa garin Konduga ne; shi ne dai yan kunar bakin-wake uku suka yi shigar-burtu a cikin su inda a haka suka Tatar da ababen fashewar da yake a jikin su”. Inji majiyar.
Injiniya Satomi ya kara da cewa “haka kuma baki dayan wadanda wannan ja’ifar ta rutsa dasu an kwashe su zuwa babbar asibitin Maiduguri, wadanda kuma al’amarin su baiyi tsanani ba an mika su asibitin Konduga domin duba su”.Ya bayyana.
Yayin da adadin da Bello Dambatta, jami’in bada agajin gaggawa na musamman dake garin Konduga lokacin da wannan al’amarin ya faru ya bayar ya sha babban dana shugaban hukumar agajin jihar Borno ya bayar. Dambatta ya shaidar wa manema labarai cewa mutane 15 ne suka rasa rayukan su, inda mutane 43 suka samu mabbantan raunuka., Dambat
Rundunar yan-sandan jihar Borno ta ta bakin mai magana da yawun rundunar; DSP ISuku Bictor, da faruwar wannan al’amarin tare da bayyana alkaluman wadanda suka rasa rayukan su da suka hada har da wani shahararren malamin addinin musulunci kuma babban limamin garin.
Mista Bictor Isuku ya bayyana cewa“jiya da safiyar ranar lahadi wasu yan kunar bakin-wake wadanda muke kyautata zaton yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Kurumari mai tazarar kilomita 14 a gabashin karamar hukumar Magumeri. Yayin da mutane hudu suka mutu ciki harda Limamin garin.
“Yayin da kuma a yau litinin, shima da safiyar ranar litinin da kimanin karfe 10 da miti 50, wasu karin yan kunar bakin-wake maza biyu da mace daya suka kai hari wurare daban dababan a kauyen Mashemari na karamar hukumar mulkin Konduga. Inda mutane 13 suka mutu kuma 16 suka samu raunuka a cikin harin”. Ta bakin mai magana da yawun rundunar tsaron.