Yusuf Shuaibu" />

’Yan Kungiyar Asiri Sun Shiga Hannu Bisa Mutuwar Mutum Daya

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta bayyana cewa, ta cafke ‘yan kungiyar asiri har guda 86, wadanda suka addabi yankunan Adamo da Imota da kuma Ijede da ke cikin garin Ikorodu. Mutum daya ne aka harbe har lahira, yayin da mutane da dama suka ji rauni a lokacin wata arangamar ‘yan kungiyar asiri wanda ya afku a yankin Benson da ke cikin garin Ikorodu a ranar Lahadi da misalin karfe 6.45 na safe.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, rundunar ‘yan sanda ta musamman wanda kwamishinan ‘yan sandar jihar, Hakeem Odumosu ya kafa, sun sami nasarar cafke mutum 65 wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a cikin garin Ikorodu wadanda suka addabi yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bala Elkana, ya bayyana cewa, a ranar Lahadi tawagar jami’an ‘yan sanda sun kama ‘yan kungiyar asiri fiye da guda 21. Ya kara da cewa, za a gurfanar da su a gaban kuliya. Elkana ya ce, “a ranar 25 ga watan 2020 da misalin karfe shida na safe, rundunar ‘yan sanda ta musamman wanda kwamishinan ‘yan sandar Jihar Legas, Hakeem Odumosu, sun samu nasarar kama mutum 21 wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a yankin Adamo da ke garin Imota.

“Wadanda ake zargin mambobin kunsiyar asiri ne guda biyu masu hamayya da kuna da ake kira da suna Aiye da kuma Eiye confraternities, sun fito ne daga yankin Emure zuwa Adamo, inda su ka je suka addabi mazauna yankin Adamo da kewaye. An samu nasarar gudanar da wannan kame ne bisa hadin giwa da ‘yan sandar garin Imota da kuma rundunar ‘yan sanda ta musamman wanda kwamishinan ‘yan sandar jihar ya kafa.

An dai yi kamen ne bayan da aka samu bayanan sirri a kauyen Ijede, inda aka samu nasarar damke mutum 65 wadanda ake kyautata zaton ‘yan kungiyar a siri ne.

“An samu nasarar kwace kananan bindigogi guda 11 tare da sunkin albarusai masu yawan gaske daga hannun wadanda ake zargin. Wadanda ake tuhuma sun amince suna da hannu wajen kai farmaki wanda ya haddasa kisan kai da fashi da makami a cikin garin Ikorodu da ke Jihar Legas.

“Za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya idan aka kammala bincike. Kwamishinan ‘yan sandar jihar ya jaddada wa rundunar ‘yan sandar da su ci gaba wajen dakile ayyukan ‘yan kungiyar asiri a cikin jihar.”

A yankin Benson, ‘yan sanda sun bayyana cewa, lokacin da su ka isa wajen da lamarin ya faru, sun yi harbi sama domin kada ‘yan kungiyar asirin su sake yin wani kisan.

Wani mazaunin yankin mai suna Olugbenga, ya bayyana cewa, matarsa ita ta tayar da shi lokacin da ta ji harbe-harben da ‘yan kungiyar asiri suke yi. Ya ce, “mun tsinci kanmu cikin tashin hankali lokacin da muka ji guje-guje da ihun mutane sakamakon farmakin da ‘yan kungiyar asiri suka kawo yankin. Kafin iyalaina su san abin da ke faruwa, mun ji karar harbe-harbe sau da yawa. “An samu tashin hankali a ko’ina, mutane ba su san wajen da za su guda ba, ko da yake wasu sun gudu zuwa coci, yayin da wasu kuma suka gudu wasu yankunan domin su tsira da rayukansu. “Ba dan ‘yan sanda sun iso cikin gaggawa ba, to da mutane da yawa sun rasa rayukansu ko sun samu raunika ko kuma an lalata shaguna da dama.”

Olugbenga ya ci gaba da cewa, arangamar ‘yan kungiyar asiri tsakanin ‘yan kungiyar asiri na Eiye da na Aiye yana kara ta’azzara a yankin.

Ita ma wata mazaunin yankin mai suna Temitope, ta bayyana wa manema labarai cewa, arangamar ‘yan kungiyar asiri a garin Ikorodu yana kara karuwa. Ta bayyana cewa, idan da a ce tana da kudi, to da ta dauke iyayenta daga yankin ta kais u wani waje a Jihar Legas. “Arangamar ‘yan kungiyar asiri a yankin abin takaici ne, saboda mutane ne wadanda ba sa daraja rai mutane,” in ji ta.

A wani lamarin kuma makamancin wannan, rundunar ‘yan sanda sun sami nasarar cafke wasu mutum uku masu suna Hassan Lekan dan shekara 19 da Owolabi Seyi dan shekara 18 da kuma Ismailia Ibrahim mai shekaru 19 da haihuwa, bisa laifin yi wa mutane fashin dokiyoyinsu.

Elkana ya bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda daga yankin Ipaja su ne suka sami nasarar damke wadanda ake zargin. Ya kara da cewa, za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike. Ya ce, “A ranar Asabar 19 ga watan Junairun shekarar 2020 da misalin karfe 5.30 na yamma, ‘yan sandar yankin Ipaja sashe masu yaki da fashi da makami wanda kwamishinan ‘yan sandar jihar, CP Hakeem Odumosu ya kafa suka samu nasarar damke wasu mutum uku wadanda ake kyautata zaton masu yin fashi ne a cikoson ababan hawa masu suna Hassan Lekan dan shekara 19 da Owolabi Seyi dan shekara 18 da kuma Ismailia Ibrahim mai shekara 19 da haihuwa. “Wadanda ake zargin sun kware wajen sace wa mutane jakunnuna da wayoyin salula da kuma kudade. Suna fara gudanar da mummunan ayyukansu ne da misalin karfe hudu na dare har zuwa karfe bakwai na safe. An samu nasarar kwato kayayyaki daga hannun wadanda ake z argi kamar haka, wayoyin salula da jakankuna wadanda suka sace a hannun wasu mutane guda uku. Za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.”

Exit mobile version