Connect with us

LABARAI

‘Yan Kwadago Sun Yi Wa Karin Kudin Mai Tutsu

Published

on

  • Abin Zai kara Kantar Talauci A kasa
  • Hukumar Daidaita Farashi Ta Rasa Makama, In Ji Su

A ranar Alhamis ce, babbar kungiyar kwadago ta kasar nan NLC, ta yi fatali da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na yin karin kudin mai kamar yadda hukumar daidaita farashin mai ta kasa ta shelanta.
kungiyar kwadagon ta kuma bukaci da lallai a mayar da farashin man kamar yanda yake a baya, kungiyar ta ce yin karin farashin man a daidai wannan lokacin da ake fama da annobar Korona zai kara kashe harkokin kasuwanci ne da kuma tsananta talauci a kowane mataki a duk sassan kasar nan.
Cikin sanarwar da kungiyar ta NLC ta fitar, shugaban kungiyar Ayuba Wabba, ya yi zargin cewa yin karin farashin man Fetur din daga Naira 121 har zuwa Naira 143.80 a irin wannan lokacin da ‘yan Nijeriya da harkokin kasuwanci suke fafutukar farfadowa a sabili da matsalar da suka tsinci kansu a ciki a dalilin aukuwar annobar Korona, babban rashin nazari ne daga sashen gwamnati.
Sanarwar tana cewa, “Hukumar daidaita farashin man ta PPPRA ta rikita kanta da kanta a lokacin da ta ce karin farashin man na kwanan nan wai an yi shi ne da nufin daidaita farashin man wanda gwamnati ta tsame hannunta a cikinsa.
“Wannan sabon farashin da aka kara a kan man na fetur an shelanta shi ne ba tare da samun amincewa daga hukumar gudanarwa ta PPPRA din ba.
“Sannan kuma abin kunya ne matuka da shugaban hukumar ta PPPRA, a lokacin da yake kokarin kare karin da ba zai karu ba, sai ma ya rasa abin da zai fada ya koma yana kame-kame kawai a kokarin da yake yi na sayar da kankara a birnin Eskimo.
“Baya ga rikirkita kansa da ya yi, sai kuma hukumar ta PPPRA take ta kokarin janye tallafi a kan abin da an rigaya an janye tallafi din a kansa, hukumar ta kara wani raunin a kan rauni a lokacin da ya rika yin bayanin cewa wai hukumar ta PPPRA tamkar babban bankin kasa take (CBN), da kuma kamfanin inshora na kasa NAICOM, wanda a kowane lokaci za su yi abin da zai kare ra’ayin jama’a ne.
“Wannan shi ne iya bayanin da ke cikin maganar na shi. Duk sauran maganganun na shi sun doru ne a kan yanda hukumar ta PPPRA ke shirin tsara yanda za ta kare masu zuba jari da kuma yanda za ta kara yawan ribar da take samu.
Advertisement

labarai