‘Yan Kwallon Kafa A Ingila Za Su Kaurace Wa Su Facebook

kungiyoyin da ke buga gasar wasannin kwallon kafa a Ingila za su kaurace wa amfani da shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook da Instagram a ranar Juma’a domin neman shafukan su dauki matakan magance amfani da su da ake ana cin zarafi.

Sannan a cewar wani rahoto sa su kauracewa shafukan na tsawon kwana hudu har sai masu kula da kamfanonin sun dauki matakan da suka kamata akan yadda ake cin zarafin bakaken fata a shafukan sada zumunta.

kungiyoyin kwallon kafa na mata da na maza za su shiga wannan yajin aikin, dama hukumomin dake shirya gasanni daban daban na kasar sannan sun ce suna son nuna wa kamfanonin sadarwar fushinsu.

An sha aika wa manyan ‘yan wasa sakwannin barazana da wariyar launin fata, duk da cewa kamfanonin sun yi alkawarin daukar mataki amma har yanzu babu abinda sukayi akan lamarin da ya addabi mutane ciki har da masu kallo.

Exit mobile version