’Yan Kwamitin Bakin Kura Sun Cafke Dilan Tabar Wiwi A Bauchi

A Larabar nan da ta gabata ne, ‘yan kwamitin Unguwar Bakin Kura da ke cikin garin Bauchi su ka yi nasarar cacimo wani matashi Muhammad Sani mai safaranr tabar nan ta wiwi wacce take bugar da mashayanta.

‘Yan kwamitin sun yi nasarar kame shi ne a lokacin da ke simoggulin din tabar wiwin din domin kai ta wani kauye Durun a cikin Bauchi don saidawa ga jama’an da suke da bukatarta. An kuma kama sa ne dauke da gammo-gammo na tabar wiwi din har guda biyu shake dam da wiwi din.

Da yake bayanin yadda aka yi ya tsunduma sana’ar safaran tabar wiwi din, matashin da ya shiga hanun ya bayyana wa wakilimu cewar “Sunana Muhammad Sani, ina da zama ne a bayan Firamaren Bakaro, amma haihaffen nan unguwar ne (Inda aka kamasa, Bakin Kura). An kamani ne da tabar wiwi, amma ni gaskiya ina sha kuma ina dan saidawa ga mabukata”.

Ya ce, wani dilar tabar ne ya gayyaceshi domin ya zo ya amsa gammon wiwin din, “Ina gida sai wani dan nan unguwar mai suna Babba ya kirani ya ce min lallai na zo na karba, na ce masa ni fa ba na da kudi, ya ce na dai zo na karba. Zuwa ta kenan, sai na zo muka shiga ya bani, a she mun yi shuka a idon faraka, yan kwamiti suna kallonmu”.

Ya ce, ya tabbbatar da ya karya dokar da ta hana shan tabar wiwi, don haka nema yake neman sassauci “tabbas na san akwai dokar da ta haramta shan wannan tabar wiwin din, na yi kuskure ina son a min aikin gafara.

Sai dai kuma matashin ya nuna kaduwarsa bisa wannan lamarin, sai ya ce daga wannan ya daina, “Ina koron alfarma da su sassauta min, daga yau ba zan sake safaran tabar wiwi ba, na tuba kena, in kuma ma ba su yarda da tubana ba, su sanya ido a kaina duk ranar da na sake su sake kamani”.

Matashin ya bayyana cewar aurensa yau ko gobe “yanzu haka na bayar da sadaki da kuma kayan aure, ko yau ko gobe za a sanya mana ranar aure. Ainihun sana’ata shi ne aikin tirayenka”.

Ta fuskacin ‘yan kwamitin kuma, sun bayyana yadda suka yi suka samu nasarar, Sulaiman Aliyu mamba a cikin ‘yan kwamitin na Bakin Kuran ya bayyana cewa “muna zaune a bakin titi muna sanya ido kan yadda abubuwa suke tafiya, wajajen karfe sha daya sai wani mambanmu daga cikin lungun nan ya zo ya shaida mana cewar yana zargin wani matashi da amsar tabar wiwi, saboda haka, sai muka ga sun zo wucewa da wadda ya sayar masa Abubakar Babba”.

Dan kwamitin ya ci gaba da cewa, “Ba mu iya kaiwa ga kamasu a wannan lokacin ba, sai muka ci gaba da bibiyar sahunsu don mu ga mene ne za su yi. mun bisa daidai tashar Galabaita a cikin mota a lokadin da ke kokarin kai tafar zuwa kasuwar kauye ta Durun domin saidawa, sai muka bukaci za mu bincike jakarsa, budewar da za mu yi kawai sai muka ga damin tabar wiwi ce gammo har biyu”.

Sulaiman ya ce daga wannan wajen ne kuma suka samu nasarar kama wadda suke zargin, inda kuma suka samesa da wannan tabar, ya kuma amsa musu cewar safararta yake yi domin saidawa ga jama’a, don haka ne ‘yan kwamitin suka ce bisa horon da suka samu suna ci gaba da kokarinsu wajen tabbatar da tsaftace unguwar da kuma taimaka wa jami’an tsaro wajen kakkabe masu aikata munanan aika-aika a fadin unguwar.

Wakilinmu ya labarta mana cewar tuni ‘yan kwamitin suma hannatan wadda suka kaman ga hukumar da ke aikin hana shad a fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA reshen jihar Bauchi domin hukuntasa daidai da laifinsa.

 

Exit mobile version