Tawagar yan kwankwasiyya daga karamar hukumar Dala karkashin jagorancin Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare Galadiman Gado da masun kano sun kaiwa jagora kwankwasiya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ta’aziyya rasuwar mahaifinsa maji-dadin Kano a gidansa dake kan titin miler dake Kano.
Tawagar wacce ta kunshi tsohon.dan majalisar tarayya mai wakiltar Dala.Hon.Ali Sani Madakin gini.da dan majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Dala. hon.Nura Husaini da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na yankin.
Tawagar ta bayyana mutukar alhini da rasuwar Saleh da cewa babban rashine na Uba kaka data tafida rayuwarsa wajen hidintawa al’umma. Sannan sunyi.addu’ar Allah ayi masa rahama da aljanna kuma ya baiwa kwankwaso da dukkan iyalan marigayin hakurin rashin.
Da yake zantawa da manema labarai jagoran tawagar kwankwasiyya na Dala da sukazo ta’aziyyar.Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare.Galadiman Gado da masun Kano yace tawagar tasu daga karamar hukumar Dala sunzo ne domin yin.ta’aziyya mahaifinsa domin na rashine ga kwankwaso kadai ba ko al’ummar Madobi da jahar Kano rashine na kasa baki daya musamman in akayi la’akari da halayyarsa ta mutuntaka da son zaman lafiya a dukkan tarihin rayuwarsa.
Yace su yanzu Kwankwaso Ubane a wajensu Dan haka kowane abu na alhini data sameshi ya samesu hakama duk abin farin ciki suna tare dashi shi yasa suka zo kwansu da kwarkwatarsu domin yiwa jagora ta’aziyya da fatan Allah yayi rahama .ga Marigayi Makaman na karaye.
Alhaji Dayyabu Ahmad Maiturare.Jagoran Kwankwasiyya na karamar hukumar Dala.