Sani Hamisu" />

Yan Majalisa 164 Suke Goyan Bayan Gbajabiamila

Yan majalisa 164 ne ke goyon bayan Gbajabiamila a cikin majalisar wakilan da aka zaba a jam’iyyar APC, sun yanke shawarar marawa Mista Femi Gbajabiamila baya a matsayin wanda zai jagoran ce su.
Wadanda suka yi wannan zaben sun ce ba za su kalubalanci Shugaba Muhammadu Buhari kana baza su tsoki jam’iyyar APC ba akan wannan zabin da suka yi.
A ranar Talatar da ta gabata ne APC ta amince da cewa duk yunkurin da aka yi domin gabatar da wanda zai jagoranci wannan abun ta hanyar yin zabe to Gwamnatin shugaba Buhari tana tare da shi, an fadi haka ne lokacin da ake taron cin abinci wanda ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Amma a wajen taron na sabbin mambobin APC, a cikin wata sanarwa a wacce ta fita ranar Talata, Mista Tunji Ojo da kuma Darakta Janar, Mr Dunusun Chamberlain, sun ce “matsayar shugaban kasa a kan wannan abu shi ne mutane su zabi abinda suke so.”
Kungiyar ta ce Arewa ba zata iya samar da shugaba ba wanda zai wakilci Majalisar Dattijan ba.
Ya ce “muna kira da dukkan ‘yan jam’iyar APC da su girmama jam’iyya sannan su yi amfani da duk wani mataki da ta yanke akan wannan lamarin.
Sanarwar ta kara da cewa “kowanne memba na wannan jam’iyar ya san da cewa shima kashin baya ne na jam’iyar, sannan sanin kowa ne tana bawa kowa damar yin abinda ya ke so inda bai tsaba umarni ba. Kuma tana taimakawa ‘ya’yan jam’iyyar lokacin gudanar da zabe.
“Saboda haka muna sa ran cewa kowanne daga cikin ku zai bamu goyon baya dari bisa dari saboda Shugaban kasa ma yana tare da wannan kudirin namu na daukar Gbajabiamila a matsayin shugaban majalissar wakilai.
“Mun yi imani cewa yana da kwarewa sosai kwarewa fiye da sauran mutanen da suke neman kujerar. “
Femi shi ne ya yi matukar cancanta, wanda ya fi dacewa ya rike wannan mukamin fiye da kowanne mutum. “
“Ana zartar da cewa Shugaban kasa ya fito daga Arewa, yayin da Mataimakin sa ya fito daga Kudu ,yanzu an zartar da shugaban Majalisar Dattijai a Arewa.”
“Harkokin siyasa a wannan kasa yana samuwa ne kawai idan yan Arewa da Kudu suka hada hannu waje guda North-Central, North-West ne North da North-East ne arewa.”
Lokacin da muka zabi Shugaban kasa a Arewa, sai muka nemo mataimakin sa a Kudu to gaba daya kasar ta mu ta ginu ne a kan tushen Arewa / Kudu. “

Exit mobile version