Daga Khalid Idris Doya,
‘Yan Majalisun Dokokin jihar Bauchi biyu sun fice daga jam’iyyar APC a yau din nan.
‘Yan Majalisun sun hada da Hon. Yusuf Muhammad Bako mambar da ke wakiltar mazabar Pali da kuma Hon. Umar Yakubu da ke wakiltar mazabar Udubo.
Da ya ke tabbatar da wannan labarin, mai magana da yawun Kakakin Majalisar jihar Bauchi, Malam Abdul Burra, ya bayyana cewa ‘yan Majalisun sun shelanta fice daga APC din ne a yayin zaman Majalisar na yau Laraba
Mun nakalto cewa Hon. Bako Pali, ya ayyana komawa cikin jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar a yayin da shi kuma Hon. Udubo bai bayyana inda ya sanya a gaba zuwa yanzu ba.
Cikakken labarin na tafe…