Daga Idris Aliyu Daudawa
‘Yan majalisar wakilai ta ƙasa sun yi kira da gwamnatin tarayya da ta yi maganin halin da ake ciki na, zaman cikin fatara a faɗin Nijeriya. Bugu da ƙari an yi da gwamnatin da ta ɓullo da wasu tsare tsare waɗanda zasu iya yin maganin halin fatara wanda ake ciki.
Wannan shawarar da majalisar da yanke ya biyu bayan wani ƙuduri da wani wakili mai suna Muhammad Wudil ya gabatar agabanta mai taken,’’ Kamata ya yi a ɗauki ani ƙwaƙƙwaran mataki na fuskantar ƙakubalen fatara, ya yin da ake bukin ranar yaƙi da fatara ta duniya, a wannan shekara 2017.’’
Ɗan majalisar ya cigaba da cewar wannan ita ce shekara ta 25 da fara yaƙi da fatara ta duniya, wadda majalisar ɗinkin duniya ta ƙaddamar. Ya ce gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki a kasafin kuɗi na 2017, inda ta ɗau niyyar ɓullo da asu tsare tsare, waɗanda idan aka aiwatar da su zasu kawo ɗauki, musamman ta ɓangaren samarwa matasa ayyukan yi, mata da kuma taimakawa wajen maganin zaman banza.
Ya nuna rashin jin daɗinsa akan cewar duk matakan da gwamnatin tarayyar ta ɗauka, basu nuna cewar, ai an fara shiga wata sabuwar rayuwa ba, wajen maganin zama cikin fatara.
Da yake cigaba da bayanin cewa ya yi, majalisar ɗinkin duniya a wani rahoton data fitar dangane da Nijeriya, wanda kuma jaridar Daily Post ta wallafa, ranar 5 ga Satumba, ya nuna Nijeriya tana daga cikin ƙasar da tafi ko wacce talauci . tana mutane milyan 80 ko kuma kashi 64 na yawan jama’ar da take dasu daga cikin milyan 175, waɗanda kuma ake ganin suna rayuwa ƙasa da dalal Amurka $1.90 a rana.
Yawancin ‘yanmajalisar sun amince da ayi maganin fatara a Nijeriya, da suke nuna goyon bayansu dangane da ƙudurin, sun haɗa da Honorabul Muhammed Munguno, Ayo Omidiran, Chris Azubogu, da kuma Ossai Ossai.
‘Yanmajalisar sun yi amfani ne da wannan damar wajen kira da gwamnatin tarayya da ta sa ido da maida hankali, wajen ana amfani da kasafin kuɗin na 2017, kamar dai yadda doka ta tanada.
Ƙudurin dai ya samuamincewar ‘yan majalisar lokacin da shugaban majalisa, Yakubu Dogara ya nemi’yan majalisar su sa albarkacin bakinsu.