Khalid Idris Doya" />

‘Yan Majalisar PDP Daga Ebonyi Sun Barranta Da Sauya Shekar Gwamna Umahi

Gwamna Umahi

Gamayyar ’yan majalisar Nijeriya da ke jam’iyyar PDP daga Jihar Ebonyi sun barranta da matakin gwamnan jihar, David Umahi, ya dauka na ficewa daga cikin PDP gami da tsunduma cikin jam’iyyar APC.

A dai ranar Talata ne dai, Gwamna Umahi ya fice daga cikin jam’iyyar PDP tare da shiga APC kamar yadda rahotonni su ka zo bisa zargin PDP da tafka rashin adalci wa shiyyar kudu maso gabas.
A sanarwar manema labarai da jam’iyyar PDP ta kasa ta fitar ta karyata ikirarin gwamna Umahi na cewa ya fita daga jam’iyyar ne a dalilin rashin adalci.
Shugaban kungiyar ‘yan majalisun tarayya daga Ebonyi wato ‘Ebonyi PDP National Assembly Caucus’ kuma tsohon gwamnan jihar Ebonyi Sanata Sam Egwu, a taron manema labarai da ya kira a Abuja jiya, ya shaida cewar Umahi na da ‘yanci da damar shiga duk wata jam’iyyar da ya ke da muradi, sai dai ko kadan ba su amince da dalilin da ya bayar na cewarsa daga jam’iyyar ba.
Ya ce, ‘yan majalisun tarayya da su ka fito daga jihar ba za su taba watsi da PDP a dalilin Umahi ba.
Sanata Egwu ya ce: “Har yanzu muna cike da tunkahon mu mambobin PDP ne, jam’iyyar da muka yi tara a zaben 2029 kuma muka samu nasarar dalewa kujerunmu.”
Ya ce, gwamnan shine mutumin da ya mori PDP fiye da zato domin kuwa an nadashi shugaban PDP a jihar, kana an zabeshi a matsayin mataimakin gwamna, aka zabeshi gwamna har sau biyu a jam’iyyar PDP “Don haka bai dace ya zama butulu ba kuwa.”
“Domin warware wani shakka ko kokonto, muna farin cikin sanar da jama’a cewa babu wani mutum daya daga cikin ‘yan majalisun tarayya daga jihar Ebonyi wanda mamban PDP ne da ya sauya sheka zuwa APC, babu wanda ya bi gwamna Umahi daga cikinmu.
“Dukkanin sanatoci uku, ‘yan majalisu biyar muna alfahari da kasancewarmu mambobin PDP domin a jam’iyyar ne muka ci zabe a 2019, ba kuma za mu mance da wannan halascin ba.
“Dalilin ficewar Chief Umahi daga PDP ya rigaya ya bazu ko’ina sun ji cewa ya yi hakan ne a bisa rashin adalci daga jam’iyyar ga shiyyar kudu maso gabas na rashin zagayen tikitin tsayawa takarar shugaban kasa da mataimaki.
“Duk da muna goyon bayan lokaci ne da ya dace kudu maso gabas ta daga tutar takarar shugaban kasa a daya daga cikin manyan jam’iyyun siyasa a zaben 2023, amma duk da hakan, muna ganin rashin ladabi ne, rashin da’a da kima ne a kayyade wa’adin zagayen tikiti ga shiyoyi.
“Duk da irin gata da PDP ta yi wa Umahi baya ga nada shi shugaban PDP a jihar, mataimakin gwamna da ya zama aka zaba a PDP da gwamna har sau biyu dukka a PDP. Kuma, ‘yan uwansa biyu an zabesu a matsayin kusoshin PDP; daya Mista Austine Umahi mataimakin shugaba a shiyyar kudu maso gabas, da kuma Mista Madwell Umahi a matsayin mataimakin shugaban PDP na jiha.
“A matsayin demokradiyya, gwamna Chief Umahi yana da zabin barin wata jam’iyya da shiga wata.
“Yan majalisun da su ka shigo wannan taron manema labarun har da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta kudu),” inji Sanata Sam Egwu.
Takardar manema labarun da su ka karanta dauke da sanya hannun Sanata Sam Ominyi Egwu, Sanata Obinna Ogba, Sanata Mike Ama Nnachi, Rt. Hon. Sylbester Ogbaga, Rt. Hon. Igariwey Iduma Enwo, Rt. Hon. Chukwuma Nwazunku, Rt. Hon. Edwin Anayo and Rt. Hon. Libinus Makwe.
Daga bisani dai Sanata Sam Egwu ya gode wa uwar jam’iyyar PDP na kasa a bisa halascin da ta musu da ta ke cigaba da mu su, kana ya jinjina wa mambobin jam’iyyar da wadanda su ka zabe su, yana mai ba su tabbacin cewar su na nan a jam’iyyar da jama’a su ka zabe su har zuwa yanzu.

Exit mobile version