Mustapha Ibrahim" />

‘Yan Mata Da Samari Sun Bayyana Farin Cikinsu Na Zaftare Farashin Aure A Jigawa

‘Yan Mata Da Samari

‘Yan mata da samari a garin Danladin-Gumel da ke karamar hukumar Sule -tankarkar a jihar  Jigawa, na murna tare da shewa kan zaftare farashin aure a wanan gari, daga Naira dubu 300 zuwa Naira dubu 80. Wanda ya
hada da kudin aure (sadaki), har kuma da Naira 50,00 na shagalin ‘yan mata.

Rahotannin, sun tabatar da zaftare wannan farashi sakamakon jajircewar Shugabanin wannan gari da ke Jihar ta Jigawa, sakamakon yin babban nazari tare da yanke shawarar cewa, wannan kadai ce hanyar da za a bi domin samun mafita dangane da jinkirin da ake samu a bangaren aure tsakanin matasa da ‘yan mata na wannan gari.

A nasa jawabin, Alhaji Ado Danmadami Gumel ya bayyana cewa, sun yi gaggawar daukar wannan mataki ne, sakamakon irin matsalolin da ake samu a tsakanin matasa, musamman ta fuskar zinace-zinace bisa wahala
tare da tsadar da aure ya yi a wannan kauye nasu. Kazalika, ya yi kira ga kafatanin al’umma da su yi musu fatan alhairi da kuma ba su hadin kai, domin saukaka wannan ibada ta aure, ba ma a kauyen nasu kadai ba,
a ko’ina a fadin wannan kasa baki-daya.

Haka zalika, su ma ‘yan mata da samarin da suka bayyana nasu ra’ayin a kan wannan batu, sun nuna matukar murna da farin ciki na cewa, daga dai yanzu ko shakka babu za su daina yin kwantai, sannan su kuma samari za su daina kwanan shago.

Exit mobile version