‘Yan Mazan Jiya Za Su Taimaka Wa Rundunar Soja Wajen Kawar Da Miyagu A Jihar Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A jiya juma’a ne dai ƙungiyar ‘yan mazan jiya wato tsoffin sojoji reshen jihar Bauchi suka kai wa shugaban sojojin Birgediya ta 33 da ke Barikin Shadawanka Bauchi ziyara domin jinjina masa kan ƙoƙarinsa da kuma nemna haɗin kai da goyon bayan rundunarsa wajen taimaka musu da kuma inganta rayuwarsu musamman na ‘ya’yansu da dai sauran muhimman batutuwa da suka gudana a yayin ziyarar.

Wakilinmu ya kasance a cikin tawagar inda ya shaida mana cewar shugaban ƙungiyar ‘yan mazan jiyan Sajen Manje Idris Ɗanjuma Ningi (mai ritaya) shi ne ya jagoranci tawar kai wannan ziyarar inda a cikin jawabisa ya bayyana maƙasudin wannan ziyarar tasu, inda ya ce ziyarar dai ita ce domin su gode wa Birgediya kwamandan sojojin ta talarin da uku da ke Bauchi a bisa gudunmawar da suka baiwa ‘yan mazan jiyan a lokacin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya wanda suka gudanar na wannan shekarar “Akwai taimako da rundunar nan ta yi mana da dama muna godiya a lokacin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya, wannan ne ya kawo mu domin mu nuna godiyarmu”. Ta bakinsa

Sajen Manjan ya kuma ce sun zo wannan shalkwatan rundunar sojan ne dai domin su nuna fuskokinsu a matsayinsu na sabbin shuwagabanin ƙungiyar ‘yan mazan jiya a jihar ta Bauchi “Sannan kuma kasantuwar ba mu jima da gudanar da zaɓe na ƙungiyar ‘yan mazan jiya ba, muka zo yau domin mu nuna fuskokinmu a gareku, ku sanmu mu ma mu sanku”.

Baya ga nan kuma shugaban ‘yan mazan jiyan ya yi amfani da wannan damar wajen kai koke-kokensu a gaban shugaban sojin, inda ya buƙaci rundunar ta soja da ta take lura da su a matsayinsu na tsofin sojojin wajen samar musu da hanyoyin dogaro da kai da kuma tallafi domin rayuwarsu ta inganta ta hanyar ɗaukan ‘ya’yensu aikin soja a lokacin da aka fara ɗaukan sabbin sojoji a kowani lokaci “Muna roko da Allah da Annabi ku taimaka mu, domin ga mu ‘ya’yanmu da suka kammala makaranta babu aikin yi, sannan tsoffin sojojin nan kuma ƙarfi ya fara ƙarewa, don haka muna rokon a bamu dama a lokacin da za ɗauki sabbin sojaji a ba mu dama mu kawo ‘ya’yanmu biyu ne, uku ne, huɗu ne, ko ma zuwa goma domin su ne za su gaje mu idan ƙarfin ya ƙare domin su ci gaba da kula da rayuwarmu”. A cewar shugaban ƙungiyar tsoffin sojojin

Sai kuma ya bayyana aniyarsu na mara bawa wa rundunar ta sojan Nijeriya wajen kawar da miyagu a kowani lokaci, inda ya ce da shi da mambobinsa suna shirye su bayar da dukkanin gudunmawar da ake nema daga garesu.

A nasa jawabin, shugaban rundunar sojojin ta Shadawanka, 33 Atilare ta jihar Bauchi Birgediya Janar T.O Olowomeye ya nuna matuwar jin daɗinsa da wannan ziyarar ta tsoffin sojoji suka kawo masa da kuma rundunarsa, inda ya bayyana cewar haɗin ƙuiwar da tsoffin sojojin nan suke nema sun samu, domin kuwa tafiyar tasu duk ɗaya ne “Mu ku ne, ku ma mu ne, idan kuka ji daɗi mu ma mun ji, idan muka ji kun ji. Domin kuwa ko badinɗe ko bajima za mu zo cikinku”.

T.O Olowomeye ya ƙara da cewa “Ina son a samu alaƙar mai kyau sosai a tsakaninmu da ku, domin a cikinku akwai waɗanda sun yi aikin nan suna kuma da abubuwan da za su iya taimaka wa domin kawar da miyagu da kuma taimaka mana wajen yin aiyukanmu yanda suka dace”.

Birgediya Janar T.O ya kuma bayyana kuma bayyana cewar za su yi duk mai iyuwa wajen taimaka wa tsoffin sojojin domin inganta musu rayuwarsu da kuma samar musu da yanayin rayuwa mai fasali.

Birgediya Janar T.O Olowomeye sai ya bayyana lambar waya a garesu wanda ya ce sun fitar da wata sashi da kuma kwararrun jami’ansu waɗanda aikinsu kawai amsar rahotoni da kuma sauraron korafe-korafen jama’a, inda ya ce da buƙatar tsoffin sojojin su ke sanar da rundunarsu dukkanin wani take-taken da basu gamsu da su ba, musamman na ‘yan ta’adda domin dakile aniyarsu “Alhamdullahi ga ‘yan jarida za su taimaka mana wajen bayyana wanna, mun fitar da sashin da jama’a za su ke kai rahoto, kuma wannan lambar kyauta ne idan ka kira ta, jami’anmu suna aiki awa ashirin da huɗu suna amsar rahoto da kuma korafe-korafe, da zarar ka kira za su saurareka idan da buwatar ɗaukan mataki nan take za a ɗauka cikin gaggawa, ina fatan jama’a za su ke yi amfani da wannan lambar da muka bayar”. A cewar T.O

A hirarsa da manema labaru jin kaɗan bayan fitowarsu daga ziyarar, shugaban ƙungiyar tsoffin sojojin na jiha, Sajen Manje Idris Ɗanjuma ya shaida cewar a shirye suke su ci gaba da mara baya wa rundunar sojojin Nijeriya domin kawar da ɓata gari a cikin al’umma da kuma tabbatar da tsaro mai inganci a tsakanin al’umman jihar ta Bauchi “A lokacin ziyarar kun ji dai shugaban sojojin nan ya ba mu lambar waya da ya ce a kowani lokaci muka ga ɓata gari mu gaggauta sanar da rundunarsu domin ɗaukan matakin gaggawa, ya kuma ce a tsawon 24 wannan lambar suna aiki. Don haka za mu yi amfani da wannan damar, zan kuma ƙira dukkanin mambobina na shaida musu, duk wanda ya ga wani abun da bai gamsu da shi ba a unguwarsa ne ko garinsa ko yankinsa nan take ya sanar da gaggawa domin ɗaukan matakin da ta dace. Za mu bada dukkanin goyon baya wa rundunar soja domin tabbatar da tsaro a jihar nan da ma ƙasa baɗi ɗaya”. Ta bakinsa

Shugaban ya ce babu wanda ke fatan ya yi aiki ya mutu a cikin aiki, idan kuma mutuwa ta zo kaddara ce “Wanda ya je yaƙi ya dawo shi ne ne soja, wanda ya bai dawo ba yaƙi ta ci shi ba soja bane, don haka muke alfahari mu tsofin sojoji ne”. a cewarsa

Bayan kammala ziyarar ne kuma shugaban rundunar sojan a jihar Bauchi ya miƙa lambar yabo na kyauta ga shugaban ƙungiyar ‘yan mazan jiyan a bisa wannan ziyarar da suka kawo musu domin neman haɗin kai da kuma neman agaji don a tafi da su da kuma inganta musu rayuwa.

Exit mobile version