‘Yan Mulkin Mallaka A Kasashen Afirka (1)

Mulkin Mallaka

A cikin yardar Allah yau alkalamin mu zai karkata kan wani muhimmin batu wanda duk dan kishin nahiyar Afrika ba zai gushe ba yana alhinin irin yadda manyan kasashen duniya su ka mamaye kasashen mu na Afirka. Sannan kuma da kokarin gano yadda abin yake tare da nazarin dalilin zuwan su, tabargazar da su ka aiwatar tare da tasirinta ga rayuwar mu, tattalin arziki da addinin mu-kai har ma da tunani. Kana da tambayar kawunan mu; shin ko mun rabu da kangin wannan mulkin mallakar ko har yanzu akwai tasirinsa a rayuwarmu?

 

Kamar yadda masana sun bayyana, sun tabbatar da cewa babban musababbin da ya jawo manyan kasashen Turai su ka afka wa nahiyar Afrika tare da kafa mulkin mallaka su ne wasoson dimbin arzikin da Allah ya taskace a yankin, mamaye madafun iko da tallata addinin su.

 

Kuma hakan ya faru ne sakamakon matsin tattalin arzikin da manyan kasashen Turai su ka tsunduma a wancan lokacin, wadanda suka hada da kasashe irin Germany (Jamus), France (Faransa), Britain (Burtaniya), wanda su ka fada cikin matsananciyar fatara. Baya ga lura da su ka yi cewa wannan halin bai shafi nahiyar Afrika ba, sannan ga dimbin arziki tare da albarkatun kasa barkatai, kuma tamkar a banza, wadanda kasashen su ke bukata ruwa jallo.

 

Sannan kuma ga rahusar aikin karfi (leburanci) a nahiyar Afrika, wanda zai taimaki kasashen Turai cikin sauki su sami abinda suke nema, kamar irin su mai, hauren giwa, roba, katako, auduga da karo da makamantan su. Bugu da kari kuma wadannan kayayyaki ne masu matukar muhimmanci a wancan lokaci na gasar bunkasar tattalin arziki a manyan kasashen.

 

A hannu guda kuma, kasashen Afrikan sun fada komar yan mulkin mallaka ne biyo bayan zazzafar takaddamar yakin sama da shekaru 100 tsakanin Burtaniya da Faransa, wanda hakan ya jawo kowace tana kokarin ta mallaki kaso mai yawa a nahiyar don ta bunkasa tasirinta tare karfin fada aji a duniya.

 

A hannu guda kuma, a wajajen 1884 Berlin da Burtaniya sun gudanar da babban taro sauya fasalin tsarin mulkin mallakan jari-hujja wanda aka yi wa lakabi da “Babban Taron Congo”. Taro ne wanda kasar Portugal, hadi da shugaban kasar German- Otto bon Bismark ta kira tare da bukatar wasu daga manyan kasashen Turai su hada kai wajen fitar da matsaya guda domin ci gaba da mamaye Afrika.

 

Manyan kasashe 14 ne su ka mamaye taron a wancan lokacin su ne Austria -Hungary, Belgium, Denmark, France, Germany, Great- Britain, Italy, tare da Netherlands, Portugal, Russia, Spain,

Sweden-Norway, Turkey, da America.

 

Amma duk da hakan, a tsakanin wadannan kasashe 14, kasashen France, Germany, Great- Britain (Burtaniya), da Portugal sun fi sauran karfin fada aji a taron tare da samun kaso mafi tsoka a mamayar nahiyar Afrika.

 

Har wala yau kuma, dadin dadawa, kasashen Turai sun bayyana maitarsu wajen mamaye nahiyar Afrika ne saboda yadda su ka tsunduma cikin matsalolin rayuwa irin su rashin ayyukan yi, talauci karancin gidaje tare da kwararar mazauna yankunan karkara zuwa birane.

 

A wani rahoton da Mista Takudzwa Hillary Chiwanza ya fitar a watan Yunin 2019 ya bankado yadda aka yi wa shugabanin kasashen Afrika 22 kisan gilla, a tsakiyar ganiyar mulki, daga 1963 zuwa 2011, wanda ake alakanta shi da ci gaba da mulkar nahiyar a hanyar da manyan kasashen mulkin mallakar ke muradi. Har wala yau, binciken ya dora zargin yadda wasu daga cikin manyan kasashen ke uwa da makarbiya a ta’asar.

 

Daga 1963 aka rika yi wa wasu daga cikin shugabanin Afrika kisan dauki-dai-dai, a lokacin da suke tsakiyar ganiyar su, kuma ana kashe su da yawan wasu manyan kasashen bisa dalilin hawa kujerar naki ko kin bai wa yan mulkin mallaka hadin kai wajen aiwatar da manufofin su a nahiyar.

 

Danyen aikin yi wa shugabanin Afrika kisan dauki-dai-dai, na baya bayan nan shi ne wanda aka zartaswa shugaban kasar Libiya, Muammar Gaddafi. Haka zalika kuma, binciken ya nuna cewa ana aiwatar da wadannan kashe-kashe ta hanyar juyin mulkin soji ga shugabanin Afrika, tare da amfani da kungiyoyin leken asiri  irin su SDECE, DGSE da DST- masu alakar kut-da-kut da kasar Faransa.

 

Wannan binciken ya yi zargin cewa ya samo asali tun a lokacin Mista Charles De Gaulle, lamarin da ya share wa shugabanin kasar Faransa turbar mayar da kasashen Afrika jakar baya. Wanda idan ka lissafa adadin juyin mulkin da aka kasar Faransa ta kitsa tare da jagoranta a kasashen Afrika, a takaice wadannan kasashen ya cancanci su kai korafin su a kotun sauraren kararrakin manyan laifuka ta duniya don hukunta kasar Faransa.

 

Rahoton yace wadannan laifuka da ake zargin kasar Faransa ta aikata a bayyane suke cikin kundin tarihin, wanda kuma kafafen yada labarai daban-daban a Afirika dangane da kashe-kashe, garkame wa da wawushe kudaden kasashen Afrika. Tare da na wasu kasashen waje wadanda ke bibiyar aikace-aikacen SDECE, wajen bai wa kasar Faransa bayanan sirri tare da farfaganda maras tushe kan Afrika.

 

DGSE ita babbar cibiyar leken asirin kasar Faransa wadda aka dora wa alhakin sarrafa duk wani shugaban bakar fata a waje, kuma wannan ita ce kalmar da Faransa ke amfani da ita wajen fassara shugabanin a Afrika a matsayin mutum-mutumi wadanda ke karkashin ikon ta. Yayin da ita kuma hukumar DST (Direction of Homeland Security) ita ce ke tassarufin kamurran cikin gidan da wajen Faransa, ita ce ke bayar da bayanan tsaro kasar Faransa daga kowane irin kutsen masu shiga kasar ta barauniyar hanya.

 

Bugu da kari kuma, ita hukumar DST, yar sandan bin diddigin lamurran siyasa ce wadda ke da  hadin gwiwa da takwarorin ta wadanda suke da akidar kama-in-keta a tsarin shugabanci a fadin duniya. Sannan kuma, baya ga DGSE, DST tare da SDECE, akwai kakkafar hukumar leken asiri ta ayyukan soja, sannan kuma wannan cibiya ita ce mai alhakin yada duk wata farfaganda a duk lokacin da wata hatsaniya ta barke a kasashen Afirka.

 

Za mu ci gaba.

Exit mobile version