Gwamnan Bala Muhammad na Jihar Bauchi da yake mai da martani ga gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce ‘Yan Nijeriya basu bukatar neman izini daga Gwamnan domin zama a cikin dazukan Jihar ko kuma wani bangare na kasar.
Cece-kuce ta tsananta tsakanin gwamnoni biyun tun bayan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya da su fice daga dazukan Jihar sa, yace umurnin kuskure ne, domin kuskure ne a bayyana daukacin Yan kabila guda a matsayin masu aikata laifi sakamakon ayyukan wasu yan kalilan daga cikin su.
Bala Muhammad ya kara da cewa, kundin tsarin mulki ya baiwa gwamnatocin jihohi da tarayya amanar kula da filaye a madadin jama’a, amma ‘yan kasa basa bukatar izinin gwamnoni ko gwamnatin tarayya wajen zama a wani yanki.
Muhammed yace sashe na 41 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa yan kasa damar zama a duk inda suke so bisa ka’idar doka.