’Yan Nijeriya Da Suka Dawo Daga Libya Sun Bayyana Ukubar Da Suka Sha

Faith Oboh, 22, ita ce ta uku a cikin iyalai 12 na gidansu, wacce kuma ta rasa Mahaifiyarta tun kafin ta kammala karatunta na Sakandare.

Tana kuma daya daga cikin mutane 200 da aka dawo da su daga kasar ta Libya, yanayin ta ya alamta wacce ta fito daga wani mummunan hali.

Da take bayar da labarinta, Faith, ta bayyana cewa, asali ita mai gyaran gashi ce, amma duk da haka bakin talaucin da ya addabe ta ne ya sanya ta yanke shawarar tsallakawa kasashen wajen ta hanyar Sahara da ke kasar ta Libya a watan Disamba na shekarar 2016, domin neman yalwa.

“Daga kudin da na tara ne a sana’ar gyaran gashi na biya tsabar Naira 500,000 ga wani wanda ya tabbatar mani da shi zai iya shirya mani tafiyar nawa zuwa kasar ta Libya.

“Amma anihin manufata ita ce na isa kasar Italiya, amma abin takaicin shine muna cikin tafiya sai injin Jirgin da muke cikinsa ya samu matsala, sai da muka kwashe sama da awanni 12 tsaye cur a cikin Teku.

“A karshe dai muka buge a wani sansani na kasar ta Libya, na shiga yanayi masu ban tsoro da takaici a wannan sansanin a cikin shekara guda da na kwashe a wajen.

Ita ma da take bayyana nata labarin, Blessing Braimah, a 34, wacce take Uwa ce mai ‘ya’ya hudu, cewa ta yi, ta bar karamar sana’ar ta ne da take yi a nan domin neman mai dan gwabi a kasashen waje kamar yadda aka alkawarta mata.

A cewarta, bashin Naira dubu 600,000, ne ta ciwo domin yin tafiyar wanda take tunanin zai iya canza rayuwarta da na iyalanta.

Ta yi zargin cewa, Mijinta ne ya gudu ya kuma bar ta da yaran nata, wanda hakan ne ya tilasta mata tunanin ketarawa wajen na kasarnan.

Blessing Braimah, ta ce, lamarin a kasar ta Libya ba kyau kuma ba dadi, domin ba ka iya tabbatar da abin da zai iya samunka a kowane lokaci.

Ta ce, ita da wasu ne aka cusa su a cikin gidan yari a birnin Tripoli, inda ta bayyana rayuwa a wajen da abin tsoro kasantuwar a kullum dare da rana karan bindiga ne kawai kake ji.

Na yi ta mafarkin dawowa, amma ina ba daman hakan, domin ba waje ne da za ka je tasha kawai ka ce kana neman motar zuwa Nijeriya ba.

Shi kuwa, Osaze Imafidon, rayuwar na shi ta gama samun matsala, kasantuwar ya dawo ne a matsayin nakasasshe, wanda yake iya tafiya tare da taimakon sanduna.

Osaze Imafidon, ya ce, harbinsa aka yi da bindiga wanda hakan ne ya kai ga yanke kafar na shi guda, ya ce ba wai an harbe ni saboda aikata wani laifi ne ba, sai dai don kawai daman haka rayuwar kasar ta Libya take, hakanan kawai za ka ga suna wasa da bindigogi.

Suna iya harbinka nan take, ba kuma komai da zaran ka dan bata masu rai.

“Ba wani bakin fatan da rayuwarsa take a bakin wani abu a wajen su, hakanan za su shigo dakin ka su kwashi duk abin da suke so, ba ka kuma isa ka tanka ba, kana cewa uffan, to a bakin ranka.

 

Exit mobile version