Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yi kira ga yan Najeriya cewa su rika mika dukan korafe-korafen su ga majalisar dokokin musamman a daidai wannnan gaba wadda majalisar ke aiki a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan.
Lawan ya yi wannan kiran ne a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun mai bashi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Ola Awoniyi a ranar Laraba, a sa’ilin da wata tawaga daga jihar Enugu, mai fafutukar ganin an kirkiro jihar Adada ta kai masa ziyara a ofishin sa da ke Abuja.
Tawagar a karkashin jagorancin Chief bita Abba tare da tsohon ministan yada labarai kuma tsohon shugaban kungiyar Igbo, Chief John Nnia Nwodo.
Haka kuma, shugaban majalisar dattawan ya shaida wa tawagar cewa sun yi abinda ya kamata wajen mika bukatar su ga zauren majalisar dokokin tarayya.
“Har wala yau, mu na murna da yadda ku ka wannan bukatar ta ku ta kirkiro jihar Adada. Kuma za mu baku dukkan cikakken goyon baya da suka dace domin kikiro jihar Adada.
Yace, “bukatar ku ta na bisa kan ka’ida. Kuma yan Nijeriya su dauki damar aikin gyaran kundin tsarin mulki da majalisa ta tara wanda ta ke yi. Kuma zan yi amfani da wannan dama in roki yan Nijeriya su rinka kawo duk wasu korafe-korafe akan yadda mu ke gudanar da ayyukan majalisa, musamman a kan harkar tsaro da dukkan wani abu da suke ganin ya kamata ko bai kamata ya kasance a cikin tsarin mulki ba.”
“Wannan shi ne lokacin da ya dace a dauki wannan damar ta zuwa majalaisar dokoki ta tarayya wajen mika duk wata bukatun da ake damun su”.
A nashi bangaren, Chief Abba tare da Chief Nwodo sun bukaci taimako tare da goyon bayan shugaban majalisar da ita kanta majalisar ga bukatar su ta kirkiro jihar Adada daga jihar Enugu.